Gwamnan ya kuma bayyana cewa a farkon shekarar da muke ciki ma saida jihar ta kara albashin ma’aikatanta, inda ya kara da cewa yana da burin mayar da mafi karancin albashin N100, 000 a watan janairun 2025.
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hadarin tankar dakon man fetur a garin Majiya na jihar Jigawa a Najeriya ya kai kusan 170 yayin da fiye da mutane 60 ke ci gaba da karbar magunguna a asibitoci daban daban.
A jiya Laraba an birne fiye da mutane 140 da hatsarin fashewar tankar fetur ya rutsa dasu. Kimanin wasu mutane 90 da mummunan hatsarin ya rutsa dasu na samun kulawar likitoci a asibitoci daban-daban dake jihar.
Hakan na zuwa ne bayan da sakin ruwan da aka yi daga madatsar ruwa ta Alau ya hallaka fiye da mutane 30 tare da yin awon gaba da dubban gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Za a fara raba alluran rigakafin ga jihohin da suka fi fama da annobar, musamman ma Kebbi da Bayelsa kuma hakan zai zama kari ne akan sauran magungunan maleriyar da ake dasu.
Wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar ta ce shugabannin biyu “na gudanar da ayyukansu na kasa duk da cewa suna waje.
A cewar Gezawa ba za su bayyana sunaye ko jam’iyyun da ‘yan takarar suka fito ba yana mai cewa hurumi ne na jam’iyyun su bayyanawa jama’a idan suna so.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga al’umar jihar ta Jigawa inda ya ba da umarnin tura wata tawaga zuwa jihar don jajantawa gwamnati da al’umar jihar.S
A sakon ta’aziyar da hadimin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya fitar a yau Laraba, Shettima ya bayyana cewar, “zuciya tayi kunci saboda iyalan da wannan mummunan al’amari ya daidaita.”
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da bankin duniya ke gargadin cewar cigaba da karin farashin man fetur na iya dawo da radadin janye tallafin man fetur daya fara raguwa sabo a Najeriya.
Bidiyoyin da al’amarin ya shafa basu kai kaso 1 cikin 100 na abubuwan da aka dora a kan dandalin ba a dan tsakanin da rahoton ya bayyana.
Domin Kari
No media source currently available