Hauhawar farashin komai a Najeriya ya karu da kaso 32.70 cikin 100 a watan Satumbar daya gabata, a cewarrahoton baya-bayan nan da hukumar kididdigar ta Najeriya (NBS) ta fitar kan sauyin farashin abubuwan da mazauna birane ke amfani dasu.
Hakan ta faru ne sakamakon saukar da hauhawar farashin tayi watanni 2 a jere cikin watan Yuli da Agustan da suka gabata.
A bisa kididdigar karshen shekara zuwa watan farko na sabuwar shekara, hauhawar farashin ta karu da kaso 5.98 cikin 100 idan aka kwatanta da kaso 26.72 da aka gani a watan Satumbar 2023.
Rahoton ya wallafa cewar, “a watan Satumbar 2024, hauhawar farashin komai ya kai kaso 32.70 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Agustan daya gabace shi na kaso 32.15 cikin 100.
Idan aka nazarci hauhawar, za’a ga cewar an samu karin kaso 0.55 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda yake a watan agustan daya gabace shi.
Farashin kayan abinci na daga cikin abubuwan dake zaburar da hauhawar farashin, inda hauhawar farashin kayan abincin ta karu zuwa kaso 37.77 a watan Satumbar daya gabata, inda yayi matukar karuwa da kaso 7.13 cikin 100 daga kaso 30.64 da aka gani a makamancin wannan lokaci a bara.
Ana danganta karuwa hauhawar farashin kayan da karuwar farashin kayan abincin da mutane suka fi amafani dasu irinsu shinkafa da masara da wake da doya.
A bisa kididdigar karshen wata zuwa farkon wani watan, nan ma an samu karuwar kaso 2.54 cikin 100 a watan Satumbar daya gabata, inda ta karu da kaso 2.64 cikin 100 daga kaso 2.37 cikin 100 a watan Agustan daya gabace shi.
Dandalin Mu Tattauna