Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Jigilar Jiragen Kasa Ta Red Line A Legas


Layin Dogo Ta Red Line
Layin Dogo Ta Red Line

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da jigilar jiragen kasan kasuwanci ta Red Line a yau.

A sanarwar daya fitar a yau Talata, Sanwo-Olu yace jigilar jiragen hayar zata yi safarar al’ummar Legas kimanin dubu 500 a kowace rana ta layin dogon.

Ya kara da cewar jiragen kasan hayar zasu tashi daga yankin Agbado zuwa Oyingbo, kuma gwamnati zata cigaba da kara yawan jigilar.

A ranar 29 ga watan febrairun daya gabata Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar jigilar layin dogon mai jan launi.

“Layin dogon mai jan launin nada tsawon kilomita 27, kuma ya ratsa ta tashoshi 8 da suka hada da Oyingbo da Yaba da Mushin da Oshodi da ikeja da Agege da Iju da kuma Agbado. Ana kiyasin cewar jiragen kasan na iya jigilar al’ummar Legas kimanin dubu 500 a kowace rana sannan zamu kara yawan jigilar domin samar da sahihiyar hanyar sufuri.”

“Za’a fara jigilar fasinjoji daga Agbado da misalin karfe 6 na safiya a kowace rana, inda jirgi na 2 zai bar Iju da karfe 7.30 na safe. Ka tabbatar kana tare da katinka domin hawa jirgin.

“Kamar dai jigilar jiragen kasan na shudin layin dogo da kayayyakin more rayuwar da gwamnati ta samar, ka tuna cewar wannan aiki namu baki daya. Mu bashi mutuntawar data dace.”

Gwamnan yayi gargadin cewar ba zai lamunci barnatarwa ko jawo cikas a harkar jigilar ba, inda yace, gaba dayanmu zamu tabbatar cewar jigilar jiragen kasarmu ta kasance abar alfahari ga kowa.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG