A yau Talata, kamfanin samar da hasken lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa ana ci gaba da kokari har ma an kusa kammala gyara tsarin samar da lantarki na Najeriya da ya rushe a jiya Litinin.
A sanarwar da ya fitar a yau Talata, janar manajan sashen hulda da jama'a na TCN, Ndidi Mbah, yace wani bangare na tsarin samarda lantarkin ya samu matsala, a ranar Litinin 14 ga watan Oktoban da muke ciki da misalin karfe 6. 48 na yamma.
A cewar sanarwar, duk da cewar nan take aka soma gyaran tsarin inda tashar lantarkin ta azura ta samara goyon bayan da ake bukata domin aikin gyaran tsarin wanda yayi matukar nisa zuwa karfe 10. 24 na safiyar yau kafin ya ci karo da kalubalen da ya janyo koma baya a aikin," a cewar sanarwar.
Kamfanin ya kara da cewar tsarin ya koma aiki a shiyar Abuja da sauran cibiyoyin rarraba hasken lantarki dake fadin Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna