Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UINCEF ya ce, yara mata miliyan 370 ke fuskantar cin zarafi ko kuma fyade kafin su cika shekaru 18 da haihuwa a fadin duniya.
Wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar, ya bayyana cewa 1 daga kowadanne yara mata 8 a duniya suna fuskantar hadarin cin zarafi da fyade. Daya daga cikin matan 5 kuma suna fuskantar irin wannan barazana ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani, wanda adadinsu ya kai miliyan 650.
Rahoton na UNICEF ya kara da cewa adadin cin zarafin yara mata na ci gaba da fadada a sassan duniya, inda yara mata miliyan 79 wanda yayi daidai da kaso 22% ke fuskantar cin zarafi a kasashen nahiyar Afirka da ke kudancin Sahara, kafin cikar haihuwarsu shekaru 18.
Sai kuma kasashen da ke gabashi da kuma gabas maso kudancin Asiya, da suke da kaso 8% da adadinsu ya kai yara mata miliyan 75 ne ke fuskantar cin zarafin.
Yara mata miliyan 73 a tsakiyar Asiya da kuma kudancinta ke fuskantar irin wannan cin zarafi, kafin cikarsu shekaru 18 da haihuwa, inda kason ya kai 9%.
Tarayyar Turai da kuma arewacin Amurka na da kaso 14% da adadin su ya kai miliyan 68 na yara mata da ke fuskantar irin wannan kalubale, a cewar UNICEF.
Yara mata miliyan 45 ne a yankin Latin Amurka da Caribbean, sai kuma yara mata miliyan 29 a arewacin Afirka da yammacin Asiya, da kuma yara mata miliyan 6 a yankin Oceania, inda suke da kaso 18%,15% da kuma kaso 34% na yara mata da ke fuskantar cin zarafi da kuma fyade.
Fatima Usman, ɗaya ce daga cikin iyaye wanda ƴarta ta taɓa fuskantar irin wannan cin zarafi a Najeriya. Ta ce ta ran ta yana kuna sosai a duk lokacin da ta tuna da wannan al’amarin
Dakta Hauwa Babura, ɗaya ce daga cikin mata masu fafutakar kare ‘yancin yara mata a Najeriya, ta kuma jaddada ƙididdigar rahoton da UNICEF, ta fitar.
A hirarsa da Muryar Amurka, Isa Sanusi, wanda shi ne babban Daraktan kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Najeriya, ya ce, yara ma na fuskantar yawaitar fyade da cin zarafi a yankunan da ke fuskantar tashe-tashen hankula a Najeriya.
Masana na ganin daukar matakai masu tsauri ne kadai hanyar da za ta kawo karshen cin zarafin yara a duniya.
Saurari rahoton Rukaiya Basha daga Abuja, Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna