Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kasafin kudin badi (2024) a matsayin Naira tiriliyan 27.5.
Hakan ya zama kari a kan hasashen farko na kasafin da Naira tiriliyan 1.5.
Ministan kasafin kudi Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan bayan Taron Majalisa Zartarwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
Kasafin ya amince da sanya canjin dala a kan Naira 700 haka nan ita kuma gangar man fetur a kan dala 73.96.
Yanzu dai har gwamnatin na shirin mika kasafin ga majalisar dokokin tarayya don amincewa.
Fadar shugaban kasar ta ce a ranar Laraba Tinubu zai gabatar da kasafin kudin ga gamayyar Majalisar Dokokin kasar.
A zamanin gwamnatin Buhari, kasafin kudin Najeriya ya dawo aiki daga watan Janairu zuwa Disamba.
Dandalin Mu Tattauna