Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’amura Sun Tsaya Cik A Majalisun Dokokin Jihohin Najeriya Tun Bayan Da Ma’aikatan Suka Shiga Yajin Aiki


Kungiyar Ma’aikatan Majalisar Dokokin Najeriya PASAN
Kungiyar Ma’aikatan Majalisar Dokokin Najeriya PASAN

Al’amura sun tsaya cik a majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya tun bayan da ‘yayan kungiyar ma’aikatan Majalisun suka tsunduma yajin aiki a shekaranjiya Litinin. Sai dai masu sharhi na cewa yajin aikin ba shine mafita ba.

KANO, NIGERIA - Uwar kungiyar ma’aikatan dake aiki a majalisun dokokin na jihohi wato PASAN ce ta umarci ‘yayan ta su shiga wannan yajin aiki na baba ta gani biyo bayan abin data kira rashin mutunta dokar data tabbatar da ‘yancin harkokin kudi ga majalisun daga bangaren gwamnonin kasar.

Yanzu haka dai zauruka da harbobin majalisar dokokin kowace jiha a Najeriya na ci gaba da kasancewa a garkame.

A hira da Muryar Amurka shugaban Kungiyar PASAN ta kasa reshen jihar Kano Comrade Bashir Yahya ya ce “Dokar kasa ce ta fada sashi na 121 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya cewa, majalisa bangare ne mai zaman kansa haka bangaren gwamnati haka bangaren shari’a, shine muke so mu ga cewa, gwamnoni sun bari komai da komai ya dawo hannun majalisa kamar yadda doka ta fayyace kuma wannan kusan jihohi 30 na Najeriya kowane gwamna ya sanya hannu akan dokar ‘yancin gashin kai ta sha’anin kudade ga majalisar dokoki.”

Majalisar Dokoki a daya daga cikin jihohin Najeriya
Majalisar Dokoki a daya daga cikin jihohin Najeriya

Sai dai a cewar, Comrade Umar Adamu Kazaure, shugaban reshen jihar Jigawa na kungiyar ta PASAN rashin mutunta yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2021 akan wannan batu tsakanin uwar kungiyar ta kasa da zauren gwamnonin Najeriya da kuma kungiyar shugabannin majalisun dokoki ta Najeriya ne ya haifar da wannan yajin aiki na sai baba ta gani.

To amma, Hon Nasiru Garba Dantiye tsohon wakili a majalisar dokokin Najeriya, yace yajin aikin da kungiyar ta PASAN keyi na nuna raunin ‘yan majalisar dokoki na jihohi a Najeriya.” Magana ce ta cewa, ‘yan majalisa suyi Magana da gwamnoni su tabbatar da cewa, gwamnonin sun bi abin da doka ta tsara, tunda tuni wannan al’amari ya riga ya zama dokar kasa.

Masu kula da lamura dai na ganin cewa, ‘yan majalisar dokokin jihohin ne sukayi wasarere da damar su lokacin da majalisar tarayya ta so dafa musu su sami wannan ‘yanci fiye da shekaru 15 baya, wato shekaru kalilan bayan da ita majalisar dokokin ta kasa ta samu na ‘yancin daga fadar shugaban kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Al’amura Sun Dakata A Majalisun Dokokin Najeriya Tun Bayan Da Ma’aikatan Suka Shiga Yajin Aiki.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG