Gwamnatin Biden ta soki matakin China na kakaba takunkumi kan wasu jami’an gwamnatin Trump a ranar Laraba, mintoci kadan bayan rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka na 46.
Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Amurka, USAGM ya sauka da yammacin jiya Laraba bisa bukatar gwamnatin Shugaba Joe Biden, jim kadan bayan da Biden ya hau mulki.
A karon farko cikin shekaru sama da goma jam'iyyar Democrat ta Amurka ta samu rinjaye a dukkan Majalisun Amurka.
Sabon shugaban Amurka ya soke dokokin dake hana ‘yan wasu kasashen musulmai da wasu kasashen Afirka shiga Amurka.
An rantsar da Dan Jam’iyyar Democrat Joe Biden, a yau Laraba a matsayin shugaban Amurka na 46 a Majalisar Amurka.
Ku kalli Shan Rantsuwar Joseph R. Biden da Kamala D. Harris da Za’a yi a Washington. Ranar Laraba 20 ga Watan Janairu Daga Karfe 11:30 na Safe Agogon Washington DC
Mai nazarin harkokin mulki a kasashen Afrika farfesa Boube Na Mewa na jami’ar Diof dake Dakar, Senegal ya bayyana cewa, a ganin sa zaben Trump babban kuskure ne.
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya yiwa mutane 73 afuwa tare da sauya hukunci wasu 70.
Yayin da ake haramar rantsar da sabon Shugaban Kasa a Amurka yau, masana na cigaba da fashin baki yayin da kuma sauran jama'a ke cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan rana da kuma bukin.
Kamar yadda yakan faru duk bayan zaben Shugaban kasa, yau ma za a rantsar da zababben Shugaban kasa Joe Biden da Mataimakiyarsa. Kamala Harris, a wani bukin da zai sha banban da yadda aka saba yi.
Kamar yadda aka saba yi tun shekaru da dama da su ka gabata, yau ma za a rantsar da zababben Shugaban Amurka, Joe Biden. Bukin rantsar da Shugaban Amurka na da tarihi mai tsawo.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.