Gwamnatin sabon shugaban Amurka Joe Biden zata dakatar da tsarin banbance tsakani sha’anin cikin gida da na kasashen waje da aka saba da shi a Amurka, wurin tinkarar batutuwan barazana ga tsaron kasa.
A karon farko tun bayan da aka rantsar da shi, shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya bayyana damuwar Amurka kan wasu batutuwa.
Shugaba Joe Biden ya gana da 'Yan majalisar dattawan Amurka a wanI yunkuri na cimma matsaya dangane da tallafin rage radadin COVID-19 a kasar.
Wasu ‘kusoshin jam’iyyar Republican a majalisar dattawan Amurka, sanata Marco Rubio da sanata Mitt Romney, a jiya Lahadi sun nuna rashin amincewar su da shirin sabuwar shari’ar sake tsige tsoho shugaban Amurka Donald Trump.
Firai ministan Birtaniya Boris Johnson ya fadawa shugaba Joe Biden cewa, a shirye yake ya bude sabon babi a yarjejeniyar kasuwancin Amurka da Birtaniya.
Rahotannin sun nuna cewa cutar coronavirus ce ta yi sanadiyar mutuwar Larry King, wanda shirinsa na "Larry King Live" na gidan talabijin din CNN ya tattaro miliyoyin 'yan kallo daga fadin duniya.
Ana kara matsawa gwamnatin Somalia lamba, yayin da ake zargi ta aika da sojojin Somalia din zuwa makwabciyar kasar Habasha domin su shiga mummunar yakin Tigray.
A ranar Litinin ne kakakin majalisar wakilai Nanacy Pelosi zata aike da bayani a kan tsige Donald Trump zuwa majalisar dattawa inji shugaban ‘yan Democrat a majalisar dattawan Chuck Schummer a jiya Juma’a.
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanya hannu a kan wasu dokokin umarnin shugaban kasa hade, da zummar samar da tallafin kudi da na abinci ga iyalai da annobar coronavirus ta yi mummunar tasiri a kan su kana zasu taimakawa ma’aikatan tarayya.
Gwamnatin Biden ta soki matakin China na kakaba takunkumi kan wasu jami’an gwamnatin Trump a ranar Laraba, mintoci kadan bayan rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasar Amurka na 46.
Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Amurka, USAGM ya sauka da yammacin jiya Laraba bisa bukatar gwamnatin Shugaba Joe Biden, jim kadan bayan da Biden ya hau mulki.
A karon farko cikin shekaru sama da goma jam'iyyar Democrat ta Amurka ta samu rinjaye a dukkan Majalisun Amurka.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.