Bakin haure sun yi murna da shirin shugaba Joe Biden na samar da hanya ta zama dan kasa a Amurka, ga kusan mutane miliyan 11 da basu da takardu, suna kyakkyawan fata a ranar Laraba, yayin da ake samun sauyi ga yadda gwamnatin Amurka ke kallo da kuma kula da su.
Sabon shugaban da aka rantsar ya sauya matsin lamba da tsauraran matakan da aka dauka tsawon shekaru hudu, kan zama dan kasa a Amurka.
Biden ya kuma bayar da umarnin zartarwa da juya wasu manufofin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, game da bakin haure, kamar dakatar da aiki a kan katangar kan iyakar Amurka da Mexico da kuma dage haramtawa mutane daga yawancin kasashen da galibinsu Musulmi ne shigowa Amurka.
Ya kuma umarci Majalisar ministocinsa da su yi aiki don kiyaye kariyar mayar da dubban daruruwan mutane da aka shiga da su Amurka tun suna yara zuwa kasashensu na asali.