Ranar Asabar 9 ga watan Janairu cibiyar samar da bayanan cutar coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins ta bada rahoton cewa mutane kusan miliyan 90 suka kamu da cutar ta coronavirus a fadin duniya.
Majalisar Dokokin Amurka ta tabbatar da nasarar Joe Biden na jam’iyyar Democrat a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba shekarar da ta gabata.
A ci gaba da rangadin da ta ke yi a cibiyoyin tsaron Najeriya, sakatariyar harkokin sojin saman Amurka, Barbara Berrett ta jagoranci wata tawagar jami'ai biyar da suka gana da ministan tsaron Najeriya a birnin Abuja.
Jami’an tsaro na musamman sun isa ginin Majalisar Dokoki yayin da dokar hana fita ta fara aiki a babban birnin Amurka, sa’o’i bayan da magoya bayan Trump suka mamaye majalisar.
Magoya bayan Shugaba Donald Trump sun mamaye ginin Majalisar Dokokin Amurka na tsawon sa’o’i a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, kafin daga bisani jami’ai su ayyana cewa al’amura sun daidaita.
A dai dai lokacin da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ke jagorantar 'yan Majalisun Amurka biyu a bikin tabbatar da kuri'un kwaleji da zababben shugaban kasa Joe Biden ya samu a zaben Nuwamba, magoya bayan Trump cikin fushi sun afkawa Majalisar tare da dakatar da wannan biki.
Mafusatan magoya bayan Shugaba Donald Trump sun fantsama cikin ginin Majalisar Dokokin Amurka a ranar Laraba a lokacin wata zanga-zanga. Turump ya yi kira ga zaman lafiya bayan an kammala rikicin amma bai bukaci magoya bayansa su watse ba. Tun daga farko ya ba su izinin zuwa titin Capitol Hill.
Har zuwa yau Laraba ba a tabbatar da jam’iyyar da za ta kasance mai rinjaye ba a majalisar dattawan Amurka a zabuka zagaye na biyu guda biyu da aka yi a jihar Georgia da ke kudancin kasar.
Da alamar su ma miyagun da ke gasa ma 'yan Najeriya aya a hannu sun kusa dandadawa, ganin yadda ake cigaba da kera ma Najeriya wasu jiragen yaki a Amurka, baya ga wasu matakan kuma da ake nazarin daukarsu.
A wata tattaunawa ta waya ta ba sabon ba, a ranar Asabar da ta gabata, Shugaban Amurka Donald Trump, ya roki jami'an zabe a jihar Georgia su samo mashi adadin kuri’un da za su bashi damar sauya sakamakon zaben kasar da aka yi wanda ya sha kayi Shugaba Joe Biden mai jiran gado kuma ya lashe.
Ana samun karin ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republican da ke goyon bayan kokarin shugaba Donald Trump na sauya sakamakon zaben kasar da aka yi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.