A ci gaba da dauke hankalin duniya da abkawa Majalisar Dokokin Kasar Amurka da kuma tsige Shugaba Donald Trump karo na biyu da ya biyo baya, masana harkokin siyasar duniya na ci gaba da tsokaci game da tasirin wannan al'amarin.
Hukumomi a Amurka sun tsaurara matakan tsaro a birnin Washington DC yayin da ya rage kwanaki a rantsar da zababben Shugaba Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46.
A karo na biyu cikin wa'adin mulkinsa na shekaru hudu Majalisar Wakilan Amurka ta sake tsige shugaban kasa Donald Trump. Kuma zai fuskanci shari'a a Majalisar Dattawa bayan sabon shugaban kasa ya fara aiki.
Sabanin yadda a baya aka yi ta muhawara, kan ko shugaban kasa zai iya yafe wa kansa laifi, yanzu abin ya zama muhimmiyar muhawara tun bayan da magoya bayan Trump su ka fusata tare da afkawa ginin Majalisar Dokokin Amurka.
A yau Laraba ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta kada kuri’a akan sake tsige shugaba Donald Trump karo na biyu, abin da ba a taba yi ba a tarihin Amurka.
A yau Laraba ne ake kyautata zaton Majlisar Wakilan Amurka mai rinjayin Democrat ke kada kuri’a a kan tsige Shugaba Donald Trump a karo na biyu, wani mataki da ya biyo bayan tarzoma da magoya bayansa suka yi a Majalisar Dokokin Kasa.
Bayanan da tambayoyi tare da Daraktan Muryar Amurka Robert Reilly, Litinin, Janairu 11, 2021
Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ce yau Litinin 'yan majalisar wakilai zasu gabatar da kudurin neman majalisar ministocin Trump ta yi amfani da dokar nan ta 25th Amendment, da ta bada dama a sauke shugaba daga mukaminsa.
'Yan jam’iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka, a jiya Lahadi, sun dau azamar tsige shugaban kasar Donald Trump, a dai-dai lokacin da wa’adin mulkinsa ke kawowa karshe.
Yayin da aka kara kama wasu daga cikin masu tarzomar da suka afka ginin majalisar dokokin Amurka ranar Larabar da ta gabata, Derrick Evans, dan majalisar wakilai a jihar West Virginia ya yi murabus daga mukaminsa saboda shiga wurin da sai da izini a majalasar.
A jiya Asabar sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce zai dage takunkumin mu’amala tsakanin jami’an Amurka da takwarorin su na kasar Taiwan, wani matakin da zai fusatar da China kana ya kara tankiya tsakanin Beijing da Washington a kwanakin karshe na mulkin shugaban Donald Trump.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.