A yau Labara ne za a rantsar da zababben Shugaban Amurka, Joe Biden na jam’iyyar Demokarat, a matsayin Shugaban Amurka na 46, a wani bikin da ya dan sha banban da yadda aka saba, saboda wasu dalilan da su ka hada da annobar corona mai yaduwa sosai a Amurka da kuma matsalar tsaro, musamman tun bnayan da wasu magoya bayan Shugaba mai jiran gado, Donald Trump, su ka abka cikin ginin Majalisar Dokokin Amurka, inda har aka rasa rayuka.
Tsoffin shugabannin Amurka da na Majalisar Dokokin kasa da sauran masu fada a ji, za su halarci bukin rantsar da Shugaban kasar; amma Shugaba Donald Trump ya ce shi ba zai halarci bukin ba. Wani mazaunin Florida anan Amurka, Dakta Nasiru Danmowa, ya ce Trump na da damar yanke shawarar kaurace ma bukin, to amma hakan ya yi hanun riga da yanda akasarin Shugabannin Amurka su ka yi a baya, in banda abin da ba a rasa ba. Ya ce halartar Shugaban wata alama ce cewa an mika mulki ga sabuwar gwamnati cikin lalama.
Dakta Danmowa ya ce baya ga matsalar corona da ta sa ala tilas za a yi akasarin harkokin bukin ta yanar gizo, da kauracewa da Shugaban mai barin gado zai yi, abu na uku da ya fito a fili shi ne matakan tsaron da ba a taba daukar irinsa ba a lokacin rantsa da Shugaban kasa. Ya ce irin shigayen da aka girke a kan hanya a Washington da kewaye sun yi kama da yadda ake daukar matakan tsaro a wurare irin Iraki. Ya ce mutane kalilan aka gayyata zuwa wurin rantsarwar saboda wadannan dalilan.
A yanzu haka dai an jibge dubban dogarawan tsaron kasa da sauran jami’an tsaro a birnin Washington DC don tabbatar da tsaro. Kuma da yammacin jiya Talata, bayan wani tankade da rairaya, an tsame 12 daga cikin dagarawan tsaron, saboda wasu shakku da ake da su kansu ganin matsalolin da aka samu da su a baya, a cewar hukumomi.
Ga Maryam Dauda da cikakken rahoton: