Mayakan kungiyar Boko Haram sun sanar da yin mubaya’a da kungiyar ISIS, 'yan sa'oi bayan tashin bama - bamai da suka hallaka sama da mutane hamsin a jihar Borno
Yara fiye da dubu daya suke karatu a wannan makarantar dake jikin sansanin 'yan gudun hijira Na Damare a Jihar Adamawa. Hedimasta da akasarin malamansu ma 'Yan gudun hijira ne daga sassa dabam dabam na Adamawa da Borno.
Iyayen 'yan matan Chibok da a ka sace sun maida martani ga gwamnati inda su ka ce sun gaji da gafara sa kuma ko kaho ba sa gani.
Bayan kwato wasu garuruwa da dakarun hadin gwiwa hade da na Najeriya su ka yi, gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakan kare aukuwar hakan.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari akan wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya, sannan suka kashe a kalla mutane 68.
Biyo bayan sakamakon zaben shekarar 2011 rikici ya barke a kusan koina a arewacin Najeriya wanda yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi
"Babu wata damuwa ko da ba sojojin Najeriya ne suka kama Abubakar Shekau ba, muddin an ci nasara" ta bakin Mr. Mike Omeri, kakakin gwamnatin Najeriya dangane da yaki da Boko Haram.
Shugaban kasar Chadi, Idirs Derby yace sojojinsa sun san inda Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram yake, a saboda haka yake kira ga shi Shekau, da yayi saranda ko kuma a kashe shi.
Kakakin rundunar sojojin Chadi ya bayyana cewa sun fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haram daga garin Dikwa tare da rasa ran sojansu guda daya a ranar 2 ga Maris din 2015.
Duk da cewa akwai barazanar kai hare-hare yayin da Najeriya ke tunkarar zabe a wannan wata mata da dama sun kudari aniyar za su fita su kada kuri'unsu.
Bayan kwato wasu yankuna daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram 'yan gudun Hijra da dama a Jihar Adamawa na komawa gida domin tunkarar zabe.
Domin Kari