Kakakin rundunar sojojin Chadi ya bayyana cewa sun fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haram daga garin Dikwa tare da rasa ran sojansu guda daya a ranar 2 ga Maris din 2015.
Duk da cewa akwai barazanar kai hare-hare yayin da Najeriya ke tunkarar zabe a wannan wata mata da dama sun kudari aniyar za su fita su kada kuri'unsu.
Bayan kwato wasu yankuna daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram 'yan gudun Hijra da dama a Jihar Adamawa na komawa gida domin tunkarar zabe.
Kungiyar Boko Haram ta sare wa wasu mutane biyu kai kamar yadda ISIS take yi tana zarginsu cewa suna leken asiri
Matar da ta gamu da ajalinta a Bauchi ba 'yar kunar bakin wake ba ce tabuwar hankali gareta.
Nijar da Kamaru da Chadi sun kaddamar da gangamin sojojin taron dangi don taimakawa Najeriya wajen yakar ‘yan kungiyar Boko Haram masu ikirarin kafa daular musulunci a yanki arewa maso gabshin Najeriya.
Gwamnatin jihar tace ta dauki ingantattun matakan da zasu tabbatar cewa ba za'a sake samun tashin hankali ba a jihar.
Wani malamin a makaranta ya sawa wasu dalibai mata cutar kanjamau a jihar Adamawa
Kwanan nan wasu jam'iyyu 23 a jihar Borno suka kira a dage zabe har zuwa watan Satumba
Ziyarar da shugaba Jonathan yakai a wasu yankunan da aka kwato daga hannun yan boko haram ya bar baya da kura.
Tun kafin 'yan Boko Haram su sace 'yan matan Chibok suka kai hari a makarantar gwamnantin tarayya dake Buni Yadi dake jihar Yobe inda suka yiwa dalibai 59 kisan gilla.
Kusan kwana goma ke nan da rundunar sojin Najeriya tayi ikirarin kwato garuruwan dake hannun 'yan Boko Haram a jihar Borno.
Domin Kari