An sake samun tashin wani bom a birnin Maiduguri, bom din ya tashi ne a kasuwar Monday, kuma ana zargin cewa an ajiye wannan bom din ne a wata jaka.
Sojojin kasar Chadi da na Najeriya da suka samu horaswa daga Sojojin Amurka da kawayenta wasu mutanen dake zaune a tafkin Chadi.
Bayan kaddamar da wani hari da su ka yi a ranar Lahadin da ta gabata, dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Nijar sun yi nasarar kwato garin Damasak da ke Najeriya.
A karshen makon da ya gabata ne Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a Najeriya ta yi mubayi'a ga kungiyar ISIS mai da'awar kafa daula musulunci. Ko ya ya masana su ke kallon wannan mataki da kungiyar ta dauka?
Sojojin kasashen Chadi, Nijar, Kamaru da Najeriya sun kai hari a kan 'yan Boko Haram.
A Karshen makon da ya gabata ne aka kai wasu jerin hare-hare inda sama da mutane 50 su ka rasa rayukansu a jahar Borno. Yanzu haka gwamnati ta ce za ta tallafawa wadanda lamarin ya rutsa da su.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun sanar da yin mubaya’a da kungiyar ISIS, 'yan sa'oi bayan tashin bama - bamai da suka hallaka sama da mutane hamsin a jihar Borno
Yara fiye da dubu daya suke karatu a wannan makarantar dake jikin sansanin 'yan gudun hijira Na Damare a Jihar Adamawa. Hedimasta da akasarin malamansu ma 'Yan gudun hijira ne daga sassa dabam dabam na Adamawa da Borno.
Iyayen 'yan matan Chibok da a ka sace sun maida martani ga gwamnati inda su ka ce sun gaji da gafara sa kuma ko kaho ba sa gani.
Bayan kwato wasu garuruwa da dakarun hadin gwiwa hade da na Najeriya su ka yi, gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakan kare aukuwar hakan.
Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari akan wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya, sannan suka kashe a kalla mutane 68.
Biyo bayan sakamakon zaben shekarar 2011 rikici ya barke a kusan koina a arewacin Najeriya wanda yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi
Domin Kari