"Babu wata damuwa ko da ba sojojin Najeriya ne suka kama Abubakar Shekau ba, muddin an ci nasara" ta bakin Mr. Mike Omeri, kakakin gwamnatin Najeriya dangane da yaki da Boko Haram.
Shugaban kasar Chadi, Idirs Derby yace sojojinsa sun san inda Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram yake, a saboda haka yake kira ga shi Shekau, da yayi saranda ko kuma a kashe shi.
Kakakin rundunar sojojin Chadi ya bayyana cewa sun fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haram daga garin Dikwa tare da rasa ran sojansu guda daya a ranar 2 ga Maris din 2015.
Duk da cewa akwai barazanar kai hare-hare yayin da Najeriya ke tunkarar zabe a wannan wata mata da dama sun kudari aniyar za su fita su kada kuri'unsu.
Bayan kwato wasu yankuna daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram 'yan gudun Hijra da dama a Jihar Adamawa na komawa gida domin tunkarar zabe.
Kungiyar Boko Haram ta sare wa wasu mutane biyu kai kamar yadda ISIS take yi tana zarginsu cewa suna leken asiri
Matar da ta gamu da ajalinta a Bauchi ba 'yar kunar bakin wake ba ce tabuwar hankali gareta.
Nijar da Kamaru da Chadi sun kaddamar da gangamin sojojin taron dangi don taimakawa Najeriya wajen yakar ‘yan kungiyar Boko Haram masu ikirarin kafa daular musulunci a yanki arewa maso gabshin Najeriya.
Gwamnatin jihar tace ta dauki ingantattun matakan da zasu tabbatar cewa ba za'a sake samun tashin hankali ba a jihar.
Wani malamin a makaranta ya sawa wasu dalibai mata cutar kanjamau a jihar Adamawa
Kwanan nan wasu jam'iyyu 23 a jihar Borno suka kira a dage zabe har zuwa watan Satumba
Domin Kari