Iyayen ‘yan makarantar Chibok da aka sace a farkon shekarar da ta gabata sun ce sai sun gani a zahiri kafin su amince da batun da gwamnati ke yi na cewa ‘ya’yansu na nan da rai.
Yayin da yake zantawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka VOA, daya daga cikin mahaifan daliban, wanda ya nemi da kada a bayyana sunansa, ya ce sun ji shelar cewa ‘ya’yansu na da rai.
“Shi Shugaban kasa ya yi alkawarin cewa a kwanan za a same su… shi ne kowa ya ke cewa sai dai an gani a kasa.” In ji mahaifin.
Game da da ko sun san inda ‘ya’yansu su ke a yanzu, sai ya ce, “ba za mu iya cewa ko su na cikin dajin Sambisa ba ko kuma ba sa ciki.”
A ranar 14 ga watan Aprilun bara ne a ka zargi ‘yan kungiyar Boko Haram da sace ‘yan matan a makarantarsu da ke garin Chibok, lamarin da ya janyo hankulan kasashen duniya.
Yanzu haka daliban sun kwashe fiye da kwanaki 320 ba tare da an ji doriyarsu a ko’ina ba.