Rahotanni daga jihohin Bauchi da Gombe na cewa an ga 'yan bindiga cikin motoci suna ratsa wasu garuruwa a jihar Bauchi da Gombe
Yau aka shiga rana ta biyu da ci gaba da kada kuri'u a wasu sassan Najeriya bayan da hukumar zabe ta kara wa'adin rufe rumfunan zabe zuwa yau lahadi.
Na’urar Card Reader na tantance masu kada kuri’a da zarar an sa hotun su ko kuma yatsunsu. Na’urar dai a zaben shekarar nan ta 2015 ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta ta fara amfani da ita.
Hukumar zaben jihar Plato ta tabbatar da rashin gudanar da zabuka a wasu rumfunan zabe ashirin a kananan hukumomi tara a jihar Plato, wadanda ta bada umurnin yin zaben a yau lahadi.
Yanzu haka dai ana nan ana tattara sakamakon zabe, amma ya zuwa lokacin da muka sami wannan rahoton akwai rumfunan da ake cigaba da jefa kuri’a a jihohin Sokoto da Kebbi.
Hukumar ‘yan sandan jihar Bauchi ta sanar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da hare-hare a kananan hukumomin Kirfi da Alkaleri a daren jiya da kuma asubar Lahadi.
Kamar a wasu jihohi a Najeriya, tun da sanyin safiya mutane suka yi tururuwa zuwa cibiyoyin zabe a jihar Adamawa inda aka fara tantance masu kada kuri’a da suka yi sammako.
Tun da missalin karfe shida na safiyar yau wasu rumfunan zabe suka fara cika da batsewa da masu jefa kuri’a a jihar Sokoto, inda suka fara janlayi tun kafin isowar malaman zabe.
A jihar Bauchi, harkar zaben yau ya gamu da cikas don a yawancin mazabun jihar an sami dan jinkiri wajen kai kayan zabe. A wasu mazabun kuma sun gamu da matsalar rashin aikin na’urar tantance katin zabe.
Tun da karfe takwas din safiyar yau Asabar daruruwan mutane su ka dinga kwararawa zuwa mazabunsu inda za a tantancesu kuma daga bisani su kada kuri’a.
Tsofaffin shugabannan Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babbangida da Janar Abdulsalami Abubakar sun yi kira ga ‘yan Najeriya game da muhimmanacin gudar da zabe lafiya da akeyi yanzu haka a Najeriya.
An kai wasu hare hare a jihohin Bauchi da Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya yayin da wani bam ya tashi a jihar Enugu da ke kudancin kasar.
Domin Kari