Dauko sojojin haya da wasu ke ikrarin gwamnati Najeriya ta yi domin yaki da kungiyar Boko Haram, na ci gaba da janyo cece-kuce. Dan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC, Farfesa Yemi Osinbajo, na daga cikin mutanen da su ka yi tsaokaci a baya-bayan nan.