Hukumar shige da fice tuni ta tura kyeyar wadanda ta cafke zuwa kasashensu ba tare da bata lokaci ba.
A jihar Borno mutane na korafin rashin cikakken tsaro a garuruwan da dakarun hadin gwiwa suka kwato daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram.
Dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Kondiga da Mafa da kuma Dikwa da ke jihar Borno, Muhammad Maina, ya ce lokaci bai yi ba da mutanen yankin za su iya komawa garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.
'Yan Gudun Hijira Baza Su Yi Zabe Ba, Najeriya, Maris 20, 2015
Makwanni kadan bayan da dakarun kasar Kamaru suka kubutar da garin Gamburo, 'yan kungiyar Boko sun sake kai hari a grin, inda suka kashe mutane 11.
Tsohon Firai Ministan Zimbabwe, Morgan Richard Tsvangirai, ya ce Najeriya na fuskantar kalubale da mayakan kungiyar Boko, ya na mai cewa duk abin da ya shafi kasar zai shafi sauran nahiyar.
Wasu kungiyoyin matan da suka jingine aiki dake jihar Borno sun koka akan kiyayyar da suka ce wani bangaren kasa na nunawa arewa.
Sojojin Cadi da Nijar Sun Kashe 'Yan Boko Haram, Maris 19, 2015
Dakarun Najeriya na ci gaba da fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram, a kokarin da su ke yi na kwato sauran garuruwan da ke hanun 'yan kungiyar.
Duk da cewa yankuna da dama ya komo hanun dakarun Najeriya a fadan da su ke yi da Boko Haram, hukumomi sun ce har yanzu babu duriyar 'yan matan Chibok.
Bayanai daga hukumomin tsaron Najeriya na nuna cewa sun sami nasarar kwato garin Bama dake jihar Borno daga hannun maharan da ake kyautata zaton ‘yan boko haram ne, garin da suka kame fiye da watanni 7 da suka wuce.
Rundunar sojojin Najeriya tayi ikirarin kwato garin Bama, gari na biyu mafi girma a jihar Borno.
Domin Kari