A ciga da samun nasara da su ke yi, dakarun Najeriya sun ce sun yi galabar kwato garin Madagali da ke Jahar Adamawa daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram.
Kasa da mako guda bayan da kungiyar Boko ta mika wuya ga kungiyar ISIS da ke kasashen Syria da Iraqi, kungiyar ta amince da mubaya'ar da ta samu, ta kuma ce hakan wata alama ce da ke nuna cewa ayyukanta na fadada zuwa sassan yammacin Afrika.
Yayinda wadanda aka kwato yankunansu ke komawa gidajensu a jihar Adamawa wata matsala ta kunno kai.
Sojoji mayakan ruwan Najeriya da na Amurka da wasu kasashe zasu fara atisahin sojojin ruwa mako mai zuwa
Sojojin kasashen waje dake yaki a Najeriya sun kara tsaurara matakan tsaro yayin da zaben shugaban kasake kunnowa inda ‘yan takarar dake kan gaba suke kunnen doki.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi ikrarin cewa kungiyar Boko Haram na samun horo daga kungiyoyin Islama da ke Gabas ta Tsakiya. Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da VOA.
Ganawar VOA da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Wannan ya biyo bayan tashin wasu bama-bamai a sananniyar kasuwar nan da ake kira Monday Market.
An sake samun tashin wani bom a birnin Maiduguri, bom din ya tashi ne a kasuwar Monday, kuma ana zargin cewa an ajiye wannan bom din ne a wata jaka.
Sojojin kasar Chadi da na Najeriya da suka samu horaswa daga Sojojin Amurka da kawayenta wasu mutanen dake zaune a tafkin Chadi.
Bayan kaddamar da wani hari da su ka yi a ranar Lahadin da ta gabata, dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Nijar sun yi nasarar kwato garin Damasak da ke Najeriya.
A karshen makon da ya gabata ne Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a Najeriya ta yi mubayi'a ga kungiyar ISIS mai da'awar kafa daula musulunci. Ko ya ya masana su ke kallon wannan mataki da kungiyar ta dauka?
Domin Kari