Wasu mahara da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen Erana ranar kasuwar garin inda suka shiga harbin mutane.
Sojoji daga Nijar da Chadi da suka kwato garin Damasak dake Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram sun gano gawarwakin mutane akalla Saba’in. Yawancinsu an yi masu yankan rago kana aka jefar dasu karkashin wata gada kamar yadda wani ganao ya shaida, Maris 20, 2015.
Munyi kwanaki muna cikin jeji, mu buya da rana, mu tafi cikin dare.
Kwamitin ya hada dukkan wakilan hukumomin tsaro.
Hukumar shige da fice tuni ta tura kyeyar wadanda ta cafke zuwa kasashensu ba tare da bata lokaci ba.
A jihar Borno mutane na korafin rashin cikakken tsaro a garuruwan da dakarun hadin gwiwa suka kwato daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram.
Dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Kondiga da Mafa da kuma Dikwa da ke jihar Borno, Muhammad Maina, ya ce lokaci bai yi ba da mutanen yankin za su iya komawa garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.
'Yan Gudun Hijira Baza Su Yi Zabe Ba, Najeriya, Maris 20, 2015
Makwanni kadan bayan da dakarun kasar Kamaru suka kubutar da garin Gamburo, 'yan kungiyar Boko sun sake kai hari a grin, inda suka kashe mutane 11.
Tsohon Firai Ministan Zimbabwe, Morgan Richard Tsvangirai, ya ce Najeriya na fuskantar kalubale da mayakan kungiyar Boko, ya na mai cewa duk abin da ya shafi kasar zai shafi sauran nahiyar.
Wasu kungiyoyin matan da suka jingine aiki dake jihar Borno sun koka akan kiyayyar da suka ce wani bangaren kasa na nunawa arewa.
Domin Kari