Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Talautar da Mutanen Mafa


Onarebul Sa'adu Gambomi yana magana da wakilin Muryar Amurka a Maiduguri
Onarebul Sa'adu Gambomi yana magana da wakilin Muryar Amurka a Maiduguri

A firar da yayi da Muryar Amurka Sa'adu Gambomi dan asalin Mafa ya bayyana irin ukubar da 'yan Boko Haram suka ganawa mutanensu da yadda suka tsiyatar da al'ummar garin gaba daya

Garin Gambomi yana da tazarar kilomita 48 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno.

Yayinda yake fira da Muryar Amurka Sa'adu Gamboni yace fitinar da suka shiga a garinsu, wato Mafa, yasa suka yi gudun hijira zuwa Maiduguri. Kawo yanzu dai sun sami wata goma sha uku suna zaune a Maiduguri.

'Yan Boko Haram sun yi kone-kone a garin har da kashe mutane arba'in da uku a lokacin da suka fita. Su 'yan Boko Haram din sun hana iyayensu da kakanninsu ficewa daga Mafan har da yi masu barazanar yankasu inda sun je Maiduguri. Haka suka rike tsoffin mutane cikin wani mugun hali.

Kwanan nan sojoji suka shiga garin suka sake kwatoshi. To saidai abun mamaki tafiyar kilomita 48 da suka soma tunda karfe shida na safe basu kai garin ba sai da yamma wajen karfe biyar duk da cewa hanyar nada kwalta mai kyau. Su 'yan Boko Haram sun binne nakiyoyi a hanyar dole ne sojoji su tsaya su tono kafin su yi gaba.

Da suka isa garin sun tarar an kone gidaje babu wurin kwana. Wadanda suka saura a garin cikin rumfuna suke kwana. Mutanen basu da abinci idan ma sun dafa 'yan Boko Haram sai su kwace. Sun yi wata hudu suna azumin dole.

'Yan Boko Haram sun sace mata da dama sun tafi dasu daji. Har yanzu ba'a san inda suke ba.Sun dauki ma matan aure da suke da sauran karfinsu suna ikirarin wai sun zama matansu.

A kan hanyarsu ta zuwa garin Mafa Sa'adu Gambomi da sojoji sun ga gawarwaki da yawa a gefen hanya wasu sun bushe wasu kuma suna ruba ba'a samu an yi masu jana'iza ba. Wasu sun zama kashi.

Duk masu garkunan shanu da dabbobi da kaji masu dimbin yawa sun yi asararsu domin su 'yan Boko Haram din suna yankasu suna ci har sai da suka tsiyatar da mutanen garin.

Yanzu dai an samu an kawo tsoffin cikin sansanin 'yan gudun hijira a Maiduguri. Yanzu su 'yan garin Mafan sun kai kusan dubu hudu kuma babu yadda zasu koma saidai an sake gina masu muhallansu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG