Rahotanni daga Najeriya na cewa sojojin kasar sun kwato garin Bama bayan fafatawa da mayakan kungiyar Boko Haram amma sai jiya ne aka sami labarin nasarar kwato garin, inji wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda da ke Maiduguri.
Ya zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan halin da garin ke ciki, don babu wani daga yankin garin da ya fadi abin da ke faruwa a garin.
Rahotanni kuma na nuna cewa wasu da mayakan suka rutsa da su sun samu sun gudo kuma galibin su tsofaffi mata da gajiyayyu.
Hukumar tsaron Najeriya ta fadi cewa ta kwato dukkan yankunan da suka fada hannun ‘yan Boko Haram dake jihar Adamawa, sai dai har yanzu garin Gwoza da ke jihar Borno na hannun ‘yan kungiyar amma jami’an tsaro sun ce suna kokarin kwato garin kamar yadda wakilin Muryar Amurka ya bayyana.
Har yanzu dai babu amo babu labarin daliban makarantar Chibok da ‘yan kungiyar suka sace. Ko a makon da ya gabata iyayen yaran sun koka ga gwamnati akan makomar ‘ya’yansu.
An shiga wata na goma sha daya ke nan da sace daliban amma har yanzu babu tabbas din kwato su, babu kuma ma wanda ya san inda suke.