A jiya laraba Amurka ta dorawa wasu mutane 3 da kamfanoni 4 takunkumi a sassan kasashen Iran, da hadaddiyar daular larabawa da Turkiyya, bisa dalilin zargin su da taimakawa wajen fitar da kayayyaki, da sayen fasahohi daga kamfanonin Amurka zuwa kasar Iran da babban bankin kasar.
Wani kwale-kwalen da ke dauke da bakin haure ya kife a gabar tekun Caribbean na Panama kusa da dajin Darien, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da ba a san adadinsu ba, kamar yadda hukumomin kasar suka fada jiya Laraba.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Laraba ya kai ziyararsa ta farko a Masar tun shekara ta 2012, inda ya gana da Shugaba Abdel Fattah al-Sisi
Tarayyar Turai EU, ta kudiri aniyar sake daura damara da ganin an sake tsugunar da tubabbun mayakan Boko Haram a kasashen yankin tafkin Chadi domin aiwatar da cikakken zaman lafiya.
An sako wata Likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a Chadi kuma tana cikin "koshashiyar lafiya," in ji ministan harkokin wajen Poland a ranar Talata.
"Isra'ila ta yi imanin cewa tana da ikon yin yadda ta ga dama," in ji ministan harkokin wajen kasar Naledi Pandor.
Isra'ila da Hamas na ci gaba da tattaunawa kan samun yarjejeniyar da ke da nufin samun tsagaita wuta da kuma 'yantar da mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza, a cewar jami'ai biyu da ke da masaniya kai tsaye kan tattaunawar.
Shugaban Amurka Joe Biden ya shiga TikTok a ranar Lahadin da ta gabata, inda a karon farko ya wallafa wani bidiyo na dakika 26 a kafar sada zumuntar ta Tiktok.
'Yan sanda a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun harba barkonon tsohuwa a ranar Litinin don tarwatsa masu zanga-zangar da suka kona tayoyi da tutocin Amurka da na Belgium a kusa da ofisoshin jakadancin kasashen Yamma da na MDD a birnin Kinshasa don nuna fushinsu kan rashin tsaro a gabashin kasar.
Ana ci gaba da neman wata likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a kudancin kasar Chadi, kamar yadda jami'ai da kafafen yada labarai a kasar Poland suka ruwaito yau Litinin.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afku a wani kauye inda ake hakar zinari a kudancin kasar a cewar hukumomin kasar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.