Isra'ila ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta yanke a makon da ya gabata, ta hanyar kashe daruruwan fararen hula a Gaza 'yan kwanaki bayan yanke hukumcin, kamar yadda Ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta fada jiya Laraba,
Wata kotun yaki da cin hanci da rashawa a Pakistan ta yanke hukuncin daure Imran Khan da matarsa Bushra Khan na tsawon shekaru 14 kowannensu, bisa zargin sayar da kyaututtukan gwamnati ba bisa ka'ida ba, jam'iyyarsa ta ce a yau, Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayar da rahoton cewa, a ranar Laraba ne wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutumin da ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu uku a wani hari da aka kai a birnin Seoul a bara.
Wani mummunan karo tsakanin wata motar bas mai hawa biyu da wata babbar motar daukar kaya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkata wasu 22 a ranar Talata a arewa maso yammacin kasar Mexico, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Gwamnatin Amurka ta ce za ta bada kyautar da zata iya kaiwa har dala miliyan biyar ga duk wanda ya bata bayanin da zai sa a kama wani tsohon jami’in Sudan da ake nema ruwa a jallo kan zargin laifukan yaki a Dafur da ya tsere daga gidan yari lokacin da yaki ya barke a shekarar da ta gabata.
Manyan kasashe masu ba da agaji da dama sun ce za su dakatar da bayar da kudade ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi na cewa ma'aikatanta na da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Kotun kolin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a ta ce dole ne Isra'ila ta kaucewa duk wani aikata kisan kiyashi a Gaza tare da samar da agajin gaggawa da ake bukata a yankin da aka yi wa kawanya.
Kamfanin makamashi na “Mainstream” a Najeriya, wanda tuni yake gudanar da manyan tashoshin samar da wutar lantarki guda biyu a kasar, ya fara gudanar da wani sabon ginin da kasar China ta samar, kusan shekara guda bayan samun wannan damar in ji kamfanin a jiya.
A ranar Laraba, wasu tankokin yaki guda biyu sun kai hari a matsugunin Majalisar Dinkin Duniya a Khan Yunis inda dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suka fake.
Iran ta fada jiya Laraba cewa, a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da aka yi juyin mulki, don shawo kan takunkumin da kasashen duniya suka kakaba mata, a daidai lokacin da Tehran ke kokarin rage maida da ita saniyar ware da aka yi, ta hanyar karfafa alaka da kasashen Afirka.
A ranar Laraba ne Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idriss Déby ya isa birnin Moscow da ke Rasha domin ganawa da Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin a fadar Kremlin.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.