Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Likitan Nan ‘Yar Kasar Poland Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Kasar Chadi - Ministan Poland


An sako wata Likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a Chadi kuma tana cikin "koshashiyar lafiya," in ji ministan harkokin wajen Poland a ranar Talata.

WASHINGTON, D. C. - Matar dai ta kasance tana aikin sa kai ne a asibitin Saint-Michel da ke yankin Tandjile na kasar Afirka ta Tsakiya, inda ake yawan yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa. Maharan da suka yi ikirarin cewa marasa lafiya ne sun yi awon gaba da ita da wata likitan kasar Mexico, kamar yadda kafar yada labarai ta Poland mai zaman kanta ta Polsat ta ruwaito.

Daya daga cikin likitocin ya tsere ne a lokacin wata hatsaniya tsakanin wadanda suka yi garkuwa da jami’an tsaron Chadi, yayin da aka tafi da matar ‘yar Poland, kamar yadda wani likitan da suke aiki tare ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. Sojojin Chadi da na Faransa suka kaddamar da nemanta tun lokacin.

Ministan harkokin wajen Poland Radek Sikorski ya wallafa wani faifan bidiyo a shafukan sada zumunta inda ya sanar da iyalan matar cewa an sako ta. Ya ce ana duba da auna lafiyarta kuma za ta dawo Poland nan ba da jimawa ba.

Ministan ya kara da cewa "Ina so in gode wa sojojin yankin da kuma kawayenmu na Faransa saboda yadda su ka taimaka a kubuto ta da ga wurin maharani”

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG