Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kakaba Takunkumi Kan Babban Bankin Iran


Ofishin Baitul Malin Amurka
Ofishin Baitul Malin Amurka

A jiya laraba Amurka ta dorawa wasu mutane 3 da kamfanoni 4 takunkumi a sassan kasashen Iran, da hadaddiyar daular larabawa da Turkiyya, bisa  dalilin zargin su da taimakawa wajen fitar da kayayyaki, da sayen fasahohi daga kamfanonin Amurka zuwa kasar Iran da babban bankin kasar.

Ofishin Baitul-Mali mai kula da kadarorin dake ketare, ya ce gungun masu gudanar da sayayyar suna fitar da fasahohin Amurka ne domin amfani da su a babban bankin kasar, lamarin da yayi karan tsaye ga takunkuman da Amurkan ta dora.

Wasu daga cikin kayayyakin da babban bankin na Iran ke bukata, kayyaki ne da aka kasafta a matsayin kayyakin yada labarai na tsaro dake da muhimmanci ga tsaron kasa da kula da ayyukan ta’addanci na sashen cinikayya, a cewar Baitul-Malin.

Babban bankin kasar Iran ya taka muhimmiyar rawa wajen bayar da tallafin kudi ga dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kungiyar Hizbullah, in ji sakataren Baitul-Malin kasar, Brian E. Nelson, ya kara da cewa, su ne manyan masu ruwa da tsaki guda biyu da ke da niyyar kara dagula zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiyar.".


"Amurka za ta ci gaba da yin amfani da duk wata hanya da ta dace wajen dakile yunkurin gwamnatin Iran na sayo fasahohin Amurka masu muhimmanci," in ji shi.

Takunkumin ya toshe damar shiga da kadarorin Amurka da asusun banki tare da hana mutanen da kamfanoni da abin ya shafa, yin kasuwanci da Amurkawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG