Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Hamas Na Ci Gaba Da Tattaunawar Sakin Wadanda Aka Yi Garkuwa Da Su Da Tsagaita Wuta


Ira’ila da Hamas
Ira’ila da Hamas

Isra'ila da Hamas na ci gaba da tattaunawa kan samun yarjejeniyar da ke da nufin samun tsagaita wuta da kuma 'yantar da mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza, a cewar jami'ai biyu da ke da masaniya kai tsaye kan tattaunawar.

WASHINGTON, D. C. - Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gudanar da muhimman tarurruka a yau Talata tsakanin bangarorin yankin a babban birnin kasar Egypt.

Ana ci gaba da tattaunawar ko da yake har yanzu Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a kudancin Gaza a garin Rafah, inda Falasdinawa miliyan 1 da dubu 400 suka tsere don neman mafaka daga fada a wasu wurare.

Jami'an kiwon lafiya na kasar Isra'ila sun bayyana cewa, an kubutar da wasu fursunoni biyu da aka yi garkuwa da su da aka kai wani mummunan harin amma kuma a garin da ke kan iyaka da Masar, harin ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 74.

Isra’ila-Falasdinawa
Isra’ila-Falasdinawa

Yarjejeniyar za ta bai wa mutanen Gaza jinkirin da suke bukata daga yakin, wanda yanzu a cikin wata na biyar, da kuma ba da 'yanci ga akalla wasu mutane 100 da ake tsare da su a Gaza. A yayin da ake ci gaba da gwabzawa, kokarin da Qatar, Amurka da Masar suka shiga na ganin an cimma matsaya ya ci tura, sakamakon sabanin ra'ayi na Hamas da Isra'ila.

Yakin ya yi barna mara misaltuwa a zirin Gaza, inda aka kashe sama da mutane 28,000, sama da kaso 70 cikin dari na mata da kananan yara, a cewar jami’an kiwon lafiya na yankin.

Isra’ila-Falasdinawa
Isra’ila-Falasdinawa

Rikicin na Isra'ila ya lalata yankuna da dama, kusan kaso 80 cikin dari na al'ummar kasar sun rasa matsugunansu kuma bala'in jin kai ya jefa sama da kashi daya bisa hudu na Falasdinawa a Gaza ga yunwa.

Netanyahu
Netanyahu

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin ci gaba har sai an samu "cikakkiyar nasara," kuma ya dage cewa matsananciyar matsin lamba na karfin soja zai tabbatar da 'yancin 'yan garkuwar, ra'ayin da abokansa suka ce aikin ceton ne ya karfafa shi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG