WASHINGTON, D. C. - Masu zanga-zangar da suka yi amfani da wata sabuwar dabara ta kai hari kan ofisoshin jakadanci, sun ce kasashen Yamma suna goyon bayan makwabciyarta Rwanda, wadda ake zargi da marawa 'yan tawayen M23 da Tutsi ke jagoranta, wadda ci gabanta ke barazana ga birnin Goma mai mahimmanci a gabashin kasar.
Rwanda dai ta musanta zargin, Kongo, gwamnatocin kasashen yammacin duniya da suka hada da Amurka da Belgium, da kuma wata kungiyar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce kungiyar 'yan tawayen na cin gajiyar tallafin da Rwanda ke bayarwa.
Duk da cewa an tsaurara matakan tsaro bayan harin da aka kaiwa jami'an Majalisar Dinkin Duniya da motoci a ranar Asabar, gungun masu zanga-zangar sun taru a ofisoshin jakadancin Amurka da Faransa da kuma ofisoshin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Congo da aka fi sani da MONUSCO.
Wasu sun yi jifa da duwatsu, inda suka yi yunkurin karya kyamarorin sa ido a daya daga cikin ofisoshin jakadancin Amurka, yayin da wasu kuma suka rika rera waka waka suna cewa "Ku bar kasarmu, ba ma son munafurncinku."
Pepin Mbndu, daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce "Al'ummar Yamma ne ke da hannu a sace-sacen da ake yi a kasarmu, Rwanda ba ta aiki ita kadai, don haka dole ne su bar kasarmu."
'Yan kallo sun yi ta murna yayin da wani mai zanga-zangar ya cire tutar Tarayyar Turai, EU daga kofar wani babban otel da ke tsakiyar birnin Kinshasa, a cewar faifan bidiyo da aka yada a kan dandalin X wadda a da aka fi sani da Twitter. Amma kamfanin dillancin labarai ta Reuters bai tabbatar da wannan faifan bidiyon ba.
Fabrice Malumba, wani direban babur da ke halartar zanga-zangar da aka yi a gaban ofishin jakadancin Amurka, ya ce "Al'ummar kasa da kasa sun yi shiru yayin da ake kashe 'yan Kwango, suna ba da kudin wa Rwanda." 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fatattakar masu zanga-zangar.
Mataimakin Firai Ministan kasar Congo kuma Ministan Harkokin wajen kasar Christophe Lutundula ya gana da jakadu da shugabannin ofisoshin diflomasiyya a birnin Kinshasa a jiya Lahadi. Ya ce za a dauki matakan tsaro domin kare wakilcin su.
Shugaban 'yan sandan Kinshasa Janar Blaise Mbula Kilimba Limba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Kamar yadda kuke gani, muna tabbatar da tsaron ofisoshin jakadanci na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango bisa yarjejeniyar Vienna."
Shekaru goma da aka kwashe ana tashe-tashen hankula a gabashin Kongo tsakanin dubunnan kungiyoyi masu dauke da makamai a kan filaye da albarkatu da kuma munanan hare-hare kan fararen hula sun kashe dubban daruruwan mutane tare da raba wasu sama da miliyan 7 da muhallansu.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna