Hare-haren da sojin Isra’ila suka kai a fadin zirin gaza sun hallaka Falasdinawa 20 a yau Litinin, ciki harda wasu mutum 6 dake zaune a tantunan da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka, a cewar jami’an bada agaji
Gwamnatin Biden ta sahalewa Ukraine yin amfani da makaman da aka kera a Amurka wajen kai hare-hare cikin Rasha, kamar yadda wasu jami’an Amurka 2 da wata majiya dake da masaniya game da shawarar suka bayyana a jiya Lahadi
Wannan farmakin aka kai da jirage marasa matuka da makaman mizile, su ne farmakin da Rasha ta kai mafi girma cikin watanni 3
Ministan harkokin wajen Japan Takeshi Iwaya zai gana da takwaran shi na Ukraine Andrii Sybiha domin ya jaddada karfin goyon bayan Japan ga Ukraine kan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.
A ranar Asabar aka kashe wasu mutane 8 aka kuma raunata wasu 17 a wani hari da aka kai da wuka a wata makaranta a gabashin China.
Shugaban Jamus Olaf Scholz a ranar Juma’a ya bukaci shugaban Rasha Vladimir Putin da ya janye dakarun shi daga Ukraine,
Kamfanin Dillancin Labaran kasar Syria SANA ya ruwaito cewa, ya jiyo daga majiyar sojan kasar cewa mutaum 15 sun mutu yayin da 16 suka jikkata, sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wasu gine-ginen gidaje da ke wajen birnin Damascus na kasar Syria a ranar Alhamis
Taron ya biyo bayan sanarwar da shugaban majalisar zartarwar ya bayar a ranar 9 ga watan Nuwamban da muke ciki ta cewa har zuwa cikar wa’adin 8 ga watan Nuwambar da aka tsayar domin mika sunaye, babu dan takarar da ya fito domin neman mukamin, in banda shugabar dake kan kujerar a halin yanzu.
A yau Laraba Joe Biden zai gana da zababben shugaban kasa Donald Trump a fadar White House bayan da shugaban na Amurka ya sha alwashin mika mulki cikin lumana ga dan jam’iyyar Republican din daya kayar a zabe shekaru 4 da suka gabata.
Babban Limamin Canterbury Justin Welby ya bayyana haka ne yayin wani taron addu’o’i da tuntuntuni.
Wani direba ya hallaka mutane 35 tare da mummunan jikkata wasu 43 yayin da ya tuka motarsa da gangan zuwa cikin dandazon jama’ar dake motsa jiki a wata cibiyar wasanni dake birnin Zhuhai na kudancin China, a cewar ‘yan sanda a yau Talata.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.