Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce na’urorin kare hare haren saman Rasha sun kakkabo wasu jirage marasa matukan 36 a wasu yankuna a yammacin Rasha cikin sa’o’I 3 kawai a yau Lahadi.
Ma'aikatan lafiya a wani asibiti sun sanar cewa dubban yara suna fama da matsanancin matsalar rashin abinci.
A ranar Asabar, kafar yada labaran Saudiyya tace, an kashe jami’an sojin kasar biyu a yayin wani hari a Yemen, akace, wanda ya kai harin na da alaka da ma’aikatar tsaron Yemen.
Isra’ila tace, zata bude sabuwar hanyar tsallakawa cikin Gaza domin ayyukan jin kai, a daidai lokacin da Amurka ke aza kaimin ganin an samar da Karin taimako ga Palasdinawa.
An dawo da 320 daga cikin gawawwakin ne daga yankin Donetsk da kuma sojoji 89 da aka hallaka kusa da garin Bakhmut, wanda Rasha ta kwace a watan Mayun bara bayan mummunar daga.
Yan Najeriya da wasu 'yan Ghana kimanin arba’in da hudu aka mayar kasashensu na asali bayan da aka samesu da laifin zama ba bisa ka’ida ba a Britaniya.
An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari na gwamnatin tarayyar Amurka bisa samunsa da hannu a wani gagarumin zamba ta yanar gizo da ya ci zarafin mutane sama da 400 a fadin Amurka wanda ya yi sanadin asarar kusan dala miliyan 20 baki daya.
Biden, wanda jigo ne a siyasar jam’iyyar Democrat na tsawon shekaru 50, ya koka da abin da ya faru da mataimakiyar shugaban kasa da ya zaba don yin takara tare da shi a 2020 don ta gaje shi.
Scholz ya kori ministan kudi kuma shugaban jam’iyyar FDP, Christian Linder biyo bayan wata doguwar tattauwanawa mai cike da takaddama wadda aka yi da nufin daidaita gibi a kasafin kudin kasar.
Shugaba Biden ya sha alwashin mika mulki ga Donald Trump cikin lumana bayan da babban abokin hamayyar siyasar tasa ya samu gagarumar rinjayen cin zabe akan Kamala Harris.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shiga sahum sauran Shugabannin duniya wajen taya Trump murnar sake zabensa a matsayin Shugaban kasar Amurka na 47.
A yau Laraba Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta kira Donald Trump domin taya shi murnar cin zaben shugaban kasa na bana, a cewar daya daga cikin hadimanta, bayan zazzafar takarar da suka yi.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.