A ranar Asabar daruruwan mazu zanga zanga a birnin Tel Aviv na kasar Isra’ila suka amayar da takaicin su kan gazawar gwamnati na cimma yarjejeniyar da zata maido sauran wadanda ake garkuwa dasu a Gaza zuwa gida.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci abokan huldar shi da su fa daina sa ido suna kallo, su hanzarta daukan matakan da suka dace na taka birki, kafin dakarun Koriya ta Arewa da aka aika Rasha su isa fagen daga.
Isra’ila ta ba da sanarwar ficewa ta gargadin ga mazauna Baalbek a gabashin Lebanon a rana ta biyu a jere.
Adadin mutanen da ambaliyar ta kashe shine mafi muni tun shekarar 1973 lokacin da aka kiyasta cewa wata ambaliya ta hallaka akalla mutane 150 a yankunan kudu maso gabashin Granada, Murcia da kuma Almeria.
“Duk birnin ya firgita, kowa na kokarin sanin inda zai je; akwai cunkoso sosai,” in ji Bilal Raad, shugaban ceto na Lebanon na shiyya Bilal Raad, kamar yadda ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
A yayin wata hira ta wayar tarho tsakaninsa da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Oktoban da muke ciki, Biden ya bayyana aniyar inganta wakilcin nahiyar Afrika a tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na ma’aikatar tsaron kasar Iran IRNA na cewa, kasar Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin soji a Tehran da kuma yammacin lardunan Khuzestan da Ilam.
Sojojin Iran sun kashe akalla ‘yan ta’adda hudu a kudu maso gabashin kasar a ranar Lahadi bayan wani kazamin harin da ‘yan ta’adda suka kai wa ‘yan sanda a ranar Asabar.
Likitocin Isra’ila sun ce wata babbar mota tayi karo da wata motar safa a daura da Tel Aviv, wanda yayi sanadiyyar jikkata mutum 35.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce zata mai da kakkausar martani biyo bayan hasashen cewa Ukraine zata kai mata farmaki da makamai masu cin dogon zango.
Isra’ila tace, ta kammala wani gagarumin hari akan Iran bayan sama da shekara guda da aka kwashe ana bata kashi, daya samo asali da wani hari da mayakan Hamas da Iran ke marawa baya suka kai kan kasar Isra’ila. a farkon watan Oktoba.
Domin Kari
No media source currently available