Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Isra'ila Sun Hallaka Falasdinawa 76 Cikin Sa'o'i 24 - Ma'aikatar Lafiyar Gaza


Hare-haren Isra'ila akan Jabalia dake arewacin Gaza
Hare-haren Isra'ila akan Jabalia dake arewacin Gaza

Hare-haren da sojin Isra’ila suka kai a fadin zirin gaza sun hallaka Falasdinawa 20 a yau Litinin, ciki harda wasu mutum 6 dake zaune a tantunan da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka, a cewar jami’an bada agaji

Wasu mutane hudu, biyu daga cikinsu yara kanana sun rasa rayukansu, a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama kan wani sansanin tantuna na Al-Mawasi dake gabar teku, da aka ware a matsayin tudun mun tsira, sannan an hallaka wasu mutum 2 a wasu matsugunan wucin gadi dake birnin Rafah na kudancin zirin a harin jirgi maras matuki, a cewar jami’an kiwon lafiya.

Bureij matsugunin Falasdinawa a tsakiyar Gaza, Nuwamba 18, 2024
Bureij matsugunin Falasdinawa a tsakiyar Gaza, Nuwamba 18, 2024

A garin Beit Lahiya dake arewacin Gaza kuma, jami’an bada agaji sun ce makami mai linzamin da sra’ila ta harba ya fada kan wani gida, inda ya hallaka akalla mutane 2 tare da jikkata wasu da dama. A jiya Lahadi, ma’aikatan bada agaji da mazauna yankin sun ce harin Isra’ila ta sama akan wani bene a yankin ya hallaka gomman mutane tare da raunata da dama.

Rundunar sojin Isra’ila, wacce ta jima tana yaki da mayakan kungiyar Hamas a zirin Gaza tun a watan Oktoban 2023, tace ta kaddamar da hare-hare akan sansanonin ‘yan ta’addan dake Beit Lahiya.

Deir Al-Balah a tsakiyar Gaza
Deir Al-Balah a tsakiyar Gaza

Wani harin Isra’ila ta sama akan wani gida a birnin Gaza ya hallaka mutane 7 tare da jikkata wasu 10, a cewar jami’an bada agaji. Daga bisani a yau Litinin, harin Isra’ila akan sansanin Nuseirat dake tsakiyar zirin Gaza ya hallaka wasu mutane 4, kamar yadda suka kara bayyanawa.

Isra’ila dai bata ce uffan ba akan hare-haren na yau Litinin.

Ma’aikatar Lafiya Ta Gaza Tace Hare-Haren Sojan Isra’ila Sun Hallaka Falasdinawa 76 A Zirin Cikin Sa’o’i 24.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG