Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Da Wuka A Wata Makaranta A Gabashin China Da Ya Halaka Mutane Da Dama


Shugaban China Xi Jinping
Shugaban China Xi Jinping

A ranar Asabar  aka kashe wasu mutane 8 aka kuma raunata wasu 17 a wani hari da aka kai da wuka a wata makaranta a gabashin China.

A ranar Asabar aka kashe wasu mutane 8 aka kuma raunata wasu 17 a wani hari da aka kai da wuka a wata makaranta a gabashin China, inda yansanda suka yi nasarar kama tsohon dalibin makarantar da ya aikata aika aikar.

Harin ya afku ne da yamma a makarantar koyon zane zane da fasaha dake birnin Yixing a yankin Jiangsu, cewar yan sandan Yixing cikin wata sanarwa da ta tabbatar da yawan wadanda harin ya rutsa da su.

Yansanda sunce, wanda ake zargin mai shekaru 21, tsohon dalibi ne a makarantar da ya kamata ya kamala karatun shi a bana, amma ya fadi a jarrabawa.

Yansanda sunce wanda ake zargin ya dawo makarantar ne domin huce haushin shi ta aikata kisan, kuma tuni ya amsa laifin shi.

Sanarwar ta kara da cewa, mai yuwuwa ne wanda ake zargin ya aikata hakan ne sakamakon rashin gamsuwa da matakin da makarantar ta dauka a kan shi. Haka zalika, yansanda na cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Yansandan birnin Yixing sunce, an tattaro ma’aikatan bayar da agajin gaggawa da dama, domin jinyar wadanda suka samu rauni da sauran wadanda harin ya rutsa da su.

Ba kasafai dai ake samun kai hari da wuka ba a China, inda suke da tsauri wajen amfani da bindiga, to amma duk da haka akwai karancin samun irin wadannan muggan hare haren na salwantar rayuka.

Ko a farkon mako wani mutum mai shekaru 62 a duniya ya kashe mutane 35 ya raunata wasu sama da 40 yayin da ya afka kan wani gungun mutane da motarsa samfurin SUV a birnin Zhuhai dake yankin kudancin China.

An cigaba da samun kai hare hare iri dabam dabam a yan watannin baya bayan nan.

Ko a watan Oktoba, wani mutum a Shanghai ya kashe mutane uku, ya kuma raunata wasu su 15 da wuka, a wani shagon sayar da kayayyaki.

Hakazalika a watan da ya gabaci wannan, anyiwa wani dan makaranta dan asalin Japan kaca kaca da saran wuka, a birnin Shenzhen dake yankin kudancin kasar mai iyaka da Hong Kong.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG