Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jamus Olaf Scholz Yayi Kira Ga Shugaban Rasha Vladimir Putin Da Ya Kawo Karshen Yakin Da Yake Yi A Ukraine


Shugaban Jamus Olaf Scholz
Shugaban Jamus Olaf Scholz

Shugaban Jamus Olaf Scholz a ranar Juma’a ya bukaci shugaban Rasha Vladimir Putin da ya janye dakarun shi daga Ukraine,

Wani mai magana da yawun gwamnatin Jamus yace, shugaba Olaf Scholz yayi magana ta wayar tarho a ranar Juma’a da shugaban Rasha Vladimir Putin, inda ya nemi Rasha ta janye dakarun ta daga Ukraine, kuma san barka, Rashan ta nuna kudurin tattaunawa kan yadda za’a samu zaman lafiya mai dorewa.

Scholz yayi Allawadai da yakin da Rasha keyi akan Ukraine, inda yayi kira ga Putin da ya kawo karshen yakin, ya janye dakarun shi, cewar mai magana da yawun gwamnatin, Steffen Hebestreit.

Fadar Kremlin tace, Putin ya shaidawa Scholz cewa, duk wata yarjejeniya da zata kai ga kawo karshen yakin da akeyi a Ukraine dole ne tazo da bukatun tsaron Rasha, da duba abinda yake na gaskiya game da bangarorin kasa."

Hebestreit ya cigaba da cewa, shugaban Jamus Olaf Scholz ya zanta da shugaban Ukraine, Velodymyr Zelensky kafin ya tattauna ta wayar tarho da shugaban na Rasha.

To sai dai duk da haka, Zelensky bai nuna wani jin dadi da kiran wayar ba. Wani faifan video da aka wallafa a shafin sa, a jiya Juma’a, Zelensky yace, a ganin shi kiran wayar rudu ne kawai.

Ya kara da cewa, ‘’wannan dama shine abinda Putin ya dade yana so: abu ne muhimmi gare shi ya ga ya sassauta kan kasancewar kasar shi saniyar ware. Komawa tattaunawa haka kara zube, ba inda zai kai. Domin abinda ya shafe gwamman shekaru yana yi ne. Hakan bai sa Rashan ta sauya komai ba a manufofin ta, ba ta yi wani abun azo a gani ba, har sai da aka kai ga wannan yakin da ake yi.

Zelensky yace, Ukraine ta fahimci yadda zata taka rawar ta game da Putin, da yadda zata gudanar da duk wata tattaunawa.

Duk wannan fadi tashin dai na zuwa ne kusan mako guda bayan gwamnatin hadin guiwar Scholz ta wargaje, inda yake fuskantar sabon zabe a farkon shekara mai zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG