Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Ukraine Akan Mamayar Da Rasha Tayi Mata


Praiministan Japan Shigeru Ishiba
Praiministan Japan Shigeru Ishiba

Ministan harkokin wajen Japan Takeshi Iwaya zai gana da takwaran shi na Ukraine Andrii Sybiha domin ya jaddada karfin goyon bayan Japan ga Ukraine kan mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.

A ranar Asabar ministan harkokin wajen Japan ya isa Kyiv domin ya tattauna batun yadda huldar sojin koriya ta Arewa ke kara Kamari tsakanin ta da Rasha, da ya hada da shigar da dubban dakaru don kamama Moscow a yakin da takeyi a Ukraine.

Ma’aikatar harkokin wajen Japan, tace, Takeshi Iwaya zai gana da takwaran shi na Ukraine Andrii Sybiha domin ya jaddada karfin goyon bayan Japan ga Ukraine akan mamayar da Rasha ta yi mata, ya kuma tattauna karin takunkumai ga Moscow.

Babban batu akan jadawalin tattaunawar shine, muhimmiyar damuwar da Tokyo ke da ita kan yadda alakar soji ke karuwa tsakanin koriya ta Arewa da Rasha.

Kamar yadda Amurka ta bayyana, nazarin bayanan sirrin koriya ta Arewa da na Ukraine, ya nuna an aike da kimanin dakarun koriya ta Arewa su 12,000 zuwa Rasha, a matsayin wani bangaren wata babbar yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasashen biyu.

Ko a makon jiya, jami’an Ukraine sunce, dakarun Ukraine da na koriya ta Arewa sun fafata, yayin da sojojin Ukraine suka harba makaman atilari kan dakarun Koriya ta Arewa a kan iyakar Kursk dake Rasha, inda Ukraine ta kaddamar da wani harin da ya shammaci Rasha a ranar 6 ga watan Agusta.

A ranar Asabar Sybiha yace, jami’an leken asirin Ukraine sunyi imanin cewa, Pyongyang na marawa mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine ne domin kwadayin samun makamai masu linzami, da na nukiliya daga Rasha, da ma sauran tsare tsaren soji.

‘’ Zurfafar hadin kan soji tsakanin Rasha, koriya ta Arewa da Iran, nayin barazana kai tsaye, ba ga Turai kawai ba, amma har da kudu maso gabashin Asiya da yankin gabas ta tsakiya,’’ ya fada a yayin wani taron manema labarai kafada kafada da Iwaya.

Ya kara da cewa, kwakkwara kuma tsararren tallafi ga Ukraine ne kadai zai iya takawa Rasha birki, da samar da ingantaccen zaman lafiya mai dorewa.

Sybiha ya kuma ce, sun tattauna irin rawar da Japan zata taka wajen aiwatar da tsarin da zai kai ga cin nasara ga Ukraine.

Hakan yazo ne gabanin wata tattaunawa da akayi da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, wanda ya shaidama manema labarai cikin wani shiri ta kafar Radion kasar cewa, zai yi dukkan mai yuwuwa wajen kawo karshen yakin a cikin shekara mai zuwa ta amfani da hanyoyin diplomasiyya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG