Da sanyin safiyar Larabar nan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fara aiki, lamarin da ya kawo dakatar da yakin da shugabannin Amurka da na Faransa suka ce zai iya samar da wata hanyar da za a sake yin sulhu a zirin Gaza.
Birtaniya ta kasance cikin shirin ko-ta-kwana a ranar litinin bayan da wata mahaukaciyar guguwa irinta ta biyu ta afkawa kasar a karshen mako, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla biyu tare da kawo cikas ga tafiye tafiye da jiragen kasa.
Kasar Isra’ila da kungiyar Hezbullah mai samun goyon bayan Iran na daf da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yau Talata, abinda zai share hanyar kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan dubban jama’a tun bayan da yakin Gaza ya tayar da shi watanni 14 da suka gabata
Zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa, a ranar farko da ya hau kan karagar mulki, zai sanya harajin kashi 25% kan duk kayayyakin da ake samu daga Mexico da Canada, da kuma karin harajin kashi 10 cikin 100 kan hajoji daga China.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ke bai wa sabbin sojojin da aka dauka domin yaki a Ukraine yafe musu bashi.
Kyodo ta ce gwamnatin shugaban Iran Masoud Pezekshkian tana neman mafita akan wannan batu da aka kasa cimma matsaya a kai kafin sabon shugaban Amurka Donald Trump ya sha rantusuwar kama aiko a watan Janairu
Wasu hare hare ta sama da Isra’ila ta kai tsakiyar Beirut a ranar Asabar ya kashe akallah mutane 15 cewar jami’ai, a daidai lokacin da ake cigaba da ganin wasu hare haren a cibiyar babban birnin Lebanon.
kasashen duniya sun kammala taro kan sauyin yanayi COPS 29 tare da rubuta jadawalin daya haifar da cecekuce, da ya bukaci kasashen da suka cigaba su jagoranci samar da dala bilyan 250 a kowacce shekara.
Dakarun Isra’ila sun kaddamar da hare hare a yankin kudancin Beirut da yankunan dake kudancin Lebanon, da sukace wurare ne da Hezbollah keda karfi.
A ranar Juma’a kafar yada labaran Rasha ta ruwaito ma’aikatar tsaron kasar na cewa, dakarun ta sun karbe iko kan wurare 5 a yaknkin gabashin Donetsk na Ukraine.
Kyiv ta rufe Majalisar Dokokinta tsawon yini guda a yau Juma’a, saboda yiyuwar kai harin makami mai linzami bayan gargadin da Shugaba Vladimir Putin ya aikewa kasashen yammacin duniya ta hanyar harba sabon makami mai linzami mai cin matsakaicin zango daka iya goya nukiliya a kan Ukraine
Kasar Rasha ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa birnin Dnipro na Ukraine a yau Alhamis, a cewar rundunar mayakan saman birnin Kyiv, a wani al’amari da za’a iya kira da karon farko na yin amafani da makaman da aka kera domin kai harin nukiliya zuwa nesa.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.