Babban Limamin Canterbury Justin Welby ya bayyana haka ne yayin wani taron addu’o’i da tuntuntuni.
Wani direba ya hallaka mutane 35 tare da mummunan jikkata wasu 43 yayin da ya tuka motarsa da gangan zuwa cikin dandazon jama’ar dake motsa jiki a wata cibiyar wasanni dake birnin Zhuhai na kudancin China, a cewar ‘yan sanda a yau Talata.
A jiya Lahadi, gwamnatin Philipines ta bada umarnin sauyawa al’ummomin kauyuka 2,500 wurin zama gabanin gagarumar guguwa ta 4 ta afkawa kasar.
Dakarun Isra’ila sun aika tankokin yaki zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat dake yammacin zirin Gaza a yau Litinin a wani sabon kutse da suka kaddamar a tsakiyar yankin, sannan jami’an kula da lafiyar Falasdinawa sun ce here-haren dakarun Isra’ila na daren Lahadi sun hallaka akalla mutane 11
Majalisar rikon kwarya da aka kafa don sake maido da tsarin dimokuradiyya a Haiti, ta sanya hannu kan wata sanarwa, inda ta kori Firai Ministan kasar na rikon kwarya, Garry Conille tare da maye gurbinsa da Alix Didier Fils-Aimé, wani dan kasuwa wanda a baya aka yi tunanin ba shi mukamin.
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce na’urorin kare hare haren saman Rasha sun kakkabo wasu jirage marasa matukan 36 a wasu yankuna a yammacin Rasha cikin sa’o’I 3 kawai a yau Lahadi.
Ma'aikatan lafiya a wani asibiti sun sanar cewa dubban yara suna fama da matsanancin matsalar rashin abinci.
A ranar Asabar, kafar yada labaran Saudiyya tace, an kashe jami’an sojin kasar biyu a yayin wani hari a Yemen, akace, wanda ya kai harin na da alaka da ma’aikatar tsaron Yemen.
Isra’ila tace, zata bude sabuwar hanyar tsallakawa cikin Gaza domin ayyukan jin kai, a daidai lokacin da Amurka ke aza kaimin ganin an samar da Karin taimako ga Palasdinawa.
An dawo da 320 daga cikin gawawwakin ne daga yankin Donetsk da kuma sojoji 89 da aka hallaka kusa da garin Bakhmut, wanda Rasha ta kwace a watan Mayun bara bayan mummunar daga.
Yan Najeriya da wasu 'yan Ghana kimanin arba’in da hudu aka mayar kasashensu na asali bayan da aka samesu da laifin zama ba bisa ka’ida ba a Britaniya.
An yankewa wani dan Najeriya hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari na gwamnatin tarayyar Amurka bisa samunsa da hannu a wani gagarumin zamba ta yanar gizo da ya ci zarafin mutane sama da 400 a fadin Amurka wanda ya yi sanadin asarar kusan dala miliyan 20 baki daya.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.