Kyiv ta rufe Majalisar Dokokinta tsawon yini guda a yau Juma’a, saboda yiyuwar kai harin makami mai linzami bayan gargadin da Shugaba Vladimir Putin ya aikewa kasashen yammacin duniya ta hanyar harba sabon makami mai linzami mai cin matsakaicin zango daka iya goya nukiliya a kan Ukraine
Kasar Rasha ta harba makamai masu linzami masu cin dogon zango zuwa birnin Dnipro na Ukraine a yau Alhamis, a cewar rundunar mayakan saman birnin Kyiv, a wani al’amari da za’a iya kira da karon farko na yin amafani da makaman da aka kera domin kai harin nukiliya zuwa nesa.
Shugabannin kungiyoyin kwadago da na jam’iyyun siyasa da jami’an fafutika masu yaki da akidar mulkin mallaka daga kasashen Afrika, Asia da na kudancin Amurka ne ke halartar wannan taro.
Alkalan kotun hukunta laifuffukan yaki ta kasa da kasa (ICC) sun bada sammacin kama firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministn tsaronsa, da shugaban kungiyar Hamas, Ibrahim Al-Masri, akan zargin aikata laifuffukan yaki da cin zarafin bil adama.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da tattaunawa kan batun tsagaita wuta a yakin Ukraine tsakaninsa da Donald Trump sai dai ya ce ba zai mayarwa Ukraine yankunanta daya mamaye ba.
Dakarun Isra’ila sun hallaka akalla mutane 19 a zirin Gaza a yau Laraba, ciki har da ma’aikatan ceto, a cewar jami’an lafiya, a dai dai lokacin da sojojin ke zafafa kutse a arewacin yankin, inda suka jefa bam kan wani asibiti tare da tarwatsa gidaje da dama.
Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya sun kawo karshen taronsu na kwanaki biyu na G20 a Rio de Janeiro, tare da bayyana goyon bayan abubuwan da suka sa a gaba a kudancin duniya: sauyin yanayi da rage talauci da kuma sanya haraji kan masu kudi.
Darajar kudin kasar China Yuan ta ragu sosai tun bayan nasarar da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya samu, kuma masana harkokin kudi na tambayar dalilin da ya sa gwamnatin kasar China ba ta daukar matakin kare darajar kudinta.
A yau Talata, shugabannin kasashe 20 mafi karfin arziki a duniya G-20 suka tattauna akan ci gaba mai dorewa da kuma komawa amfani da makamashi mai tsafta.
Harin na zuwa ne kwanaki 2 kacal bayan da gwamnatin Biden ta baiwa mahukuntan birnin Kyiv izinin yin amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango a kan wurare a cikin Rasha.
Majalisar Dinkin Duniya tace, sama da mutane miliyan 25, rabin al’ummar Sudan na bukatar agaji, sakamakon yadda fari ya mamaye wani yanki, yayinda mutane sama da miliyan 11 suka arce daga gidajen su.
Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da suka hada da Amurka da Birtaniya, sun bukaci a kai karin agajin jinkai ga Falasdinawa farar hula a Gaza ba tare da bata lokaci ba.
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.