A ranar Asabar jami’an Pakistan suka ce, wani dan kunar bakin wake yakai hari kan wani wurin shingen jami’an tsaro a wani yankin da ake dar dar a cikin shi, dake kusa da kan iyaka da Afghanistan.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sunyi gargadin cewa, aikin kwashe marasa lafiya daga yankin da yaki ya daidaita a Gaza na neman dishewa, lamarin dake jefa rayuwar dubban mutane da ya hada da yara kanana cikin hadari.
Nan bada jimawa ba yan Jam’iyar hambararriyar priministar Bangladesh Sheik Hasina ke shirin fita kan titi domin yin zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin rikon kwaryar Muhammed Yunus.
A jiya Juma’a Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya gana da firaministan kasar Lebanon, inda suka tattauna kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a kasar, a daidai lokacin da Washington ta matsa wa gwamnatin Beirut lamba kan ta dauki mataki kan kungiyar Hezbollah.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.
Harin ya zo ne bayan sa’o’i kadan da ake zargin 'yan tawaye Kurdawa sun ta da bama-bamai da kuma bude wuta a kamfanin sararin samaniya da tsaro na TUSAS.
Netanyahu, kamar yadda rahotanni suka nuna a ganawar ta tsawon sa’o’i biyu da rabi, ya shaida wa Blinken cewa kisan Sinwar zai iya kawo “kyakkyawan tasiri” wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cimma burin Isra’ila na kawo karshen mulkin Hamas.
Blinken ya isa yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda ma’aikatar harkokin waje ta sanar cikin wata sanarwa, inda ake sa ran zai tattauna muhimmancin kawo karshen yakin da akeyi a Gaza.
Sanjay Kumar Verma, wanda aka kora a ranar Litinin da ta wuce tare da wasu jami’an diflomasiyyar India biyar, ya fada a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na CTV a ranar Lahadi cewa zargin yana da alaka da bita da kullin siyasa.
Koriya Ta Arewa tayi ikirarin gano wasu tarkacen akalla jirgi mara matuki guda na sojojin Koriya Ta Kudu a babban birnin kasar Pyongyang, tare da kafa wasu hotunan jirgin da masu sharhi suka tabbatar cewa lallai na KTK ne.
An Kama wani dan asalin kasar Libya a Jamus, wanda ake zargi da kitsa kai farmaki ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Berlin sannan an alakanta shi da kungiyar IS wanda za a gabatar da shi a gaban kuliya yau Lahadi, a cewar mahukunta a Jamus.
Gwamnatin Isra’ila tace, wani jirgi mara matuki ya kaikaici gidan priminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar. An sanar da cewa, shi da mai dakin shi basa cikin gidan a lokacin da aka kai harin.
Domin Kari
No media source currently available