Rasha ta fada ranar asabar cewa, ta dakile hare haren jirage marasa matuka 47 da Ukraine tayi yunkurin kai mata hari da su, yayin da Kyiv itama ta bada rahoton kakkabo jirage marasa matuka 24 da Moscow ta yi yunkurin kai mata hari da su.
Hezbollah, wace ta rasa shugabanta da wasu manyan kwamandojin ta a wasu hare haren Isra’ila, tun lokacin da aka fara yaki a Lebanon, ta ce, ta kai farmaki da makaman missile wani sansanin sojin Isra’ila a kudancin birnin Haifa a ranar asabar, .
A yayin wani biki na kungiyar manema labarai masasa shinge a Landan. Dan Jimmy Lai, Sebastien yace mahaifin shi, wanda ke da takardar zama dan kasar Birtaniya, na cikin mawuyacin hali a inda yake a tsare kusan tsawon shekaru hudu.
Iyalan pasinjojin da suka gamu da ajalin su a hadduran jirgin saman Boeing 737 Max biyu, sun halarci zaman babban kotun kasa dake Texas, domin sauraren ba’asi, tsakanin lauyoyin su da masu gabatar da kara.
Iran tace, ta gano gawar wani janar din sojin juyin juya halin da aka kashe tare da jagoran Hezbollah Sayyadi Hassan Nasrallah a yayin wani harin da Izra’ila ta kai a watan jiya a Beirut.
Bikin wanda ke gudana duk ranar 11 ga watan Oktoba an fara gudanar da shi ne tun cikin shekarar 2012 kuma yana maida hankali ne wajen neman kara wayar da kan al’umma “akan yadda matsalolin sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da talauci ke shafar ‘ya’ya mata”
Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin makarantar.
Sanarwar bata bayyana adadin wadanda suka mutu ba sai dai tace ana amfani da cibiyar "wajen kitsawa tare da kai hare-haren ta'addanci kan sojoji dama kasar Isra'ila."
Nadal ya samu mutunci a idon duniya tare da zama gwarzon da ake koyi da shi, da kuma yin gogayya da zaratan ‘yan wasan tennis irin su Roger Federer da Novak Djokovic.
Netanyahu na nazarin zabin da yake da shi domin maida martani ga Tehran bayan da ta harba kusan makamai masu linzami 200 kan Isra’ila a ranar 1 ga Oktoba.
Hashem Safieddine, dan uwan ne ga Nasrallah kuma babban jami’in kungiyar ne da ake sa ran zai maye gurbin Nasrallah
An shirya gudanar da shagulgula a fadin Isra’ila da manyan biranen duniya domin tunawa da zagayowar ranar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan dake zirin Gaza ta kaddamar da harin, daya hallaka fiye da mutane 1, 200.
Domin Kari
No media source currently available