Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakinwake Ya Hallaka Mutane A Shingen Jami'an Tsaro A Pakistan


Wasun jami'an tsaro a Pakistan
Wasun jami'an tsaro a Pakistan

A ranar Asabar jami’an Pakistan suka ce, wani dan kunar bakin wake yakai hari kan wani wurin shingen jami’an tsaro a wani yankin da ake dar dar a cikin shi, dake kusa da kan iyaka da Afghanistan da ya kashe akalla mutane 8 da raunata wasu da dama.

Harin ya abku ne a wani mazaunin soji dake garin Mir Ali na Pakistan dake gundumar arewacin Waziristan. Ance akalla akwai sojoji 2, da jami’an yansanda su 4 da farin kaya 2 da suka rasa ran su.

Jami’an tsaro da dama a yankunan sun tabbatar da afkuwar lamarin, inda aka ruwaito cewa, dan kunar bakin waken, ya tayar da ababen fashewar ne yana kan mashin adai dai lokacin da ya isa wajen shingen da jami’an tsaron ke duba ababen hawa. Fashewar ta kuma raunata jami’an tsaro 5, inda ma’aikatan lafiya dake asibitin yankin suka ce, wadanda suka jikkatan na cikin mawuyacin hali.

An ruwaito cewa, mayakan haramtacciyar kungiyar Tehrik-i-Taliban ko TIP sun dauki alhakin kai mummunan harin. Harin yazo kwana guda bayan wani mummunan hari tsakanin mayakan a yankunan dake kewaye da arewacin Waziristan, da yayi sanadiyyar mutuwar akalla jami’an tsaron Pakistan 16 da raunata wasu da dama.

Jami’an Pakistan dai sun sanar da karuwar ban mamaki na irin hare haren bindiga dana kunar bakin wake da mayakan TIP ke kaiwa a kasar, musamman a yankin kan iyaka na Khyber Pakhtunkhwa inda arewacin Waziristan yake.

Tashin hankalin ya lashe rayukan yan Pakistan sama da 1,000, rabin su jami’an tsaro a farkon watanni 10 na wannan shekarar, cewar wata cibiyar bincike mai zaman kanta. Islamabad tace, TIP na gudanar da aikace aikacen ta a Afghanistan tamkar wata ibada, ta kuma kara kaimin hare haren a sassan kan iyaka tun bayan da gwamnatin musulunci ta Taliban ta sake karbar iko a makwabciyar kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG