An shirya gudanar da shagulgula a fadin Isra’ila da manyan biranen duniya domin tunawa da zagayowar ranar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawan dake zirin Gaza ta kaddamar da harin, daya hallaka fiye da mutane 1, 200.
Bakin haure sama da 26,600 ne suka tsallaka ruwa tsakanin Faransa da Ingila akan kananan jiragen ruwa a shekarar 2024, kamar yadda ofishin ma’aikatar cikin gida na Inglila ya sanar.
A ranar Litinin 7 ga watan Oktoban nan yakin na Isra'ila da Hamas ya cika shekara guda da barkewa.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewa, kamfanin Verizon, AT & T da Lumen suna daga cikin kamfanonin sadarwar da jaridar ta bada rahoton an yiwa kutse, da aka gano a kwanan nan tare da bayyana sunayen wasu da suke da masaniya a game da lamarin.
Ya shaida wa manema labarai cewa, “Batun da ya fi muhimmanci a yau shine tsagaita wuta, musamman a Lebanon da kuma Gaza.”
Macron ya nanata damuwarsa kan rikicin Gaza da ke ci gaba, duk da kiran da ake ta yi na a tsagaita wuta.
Hezbollah tace mayakan ta na yin fito na fito da dakarun Isra’ila a yankin kudancin kan iyakar Lebanon, inda dakarun Isra’ila sukace sun kaiwa mayakan da Iran ke marawa baya hari a wani masallaci.
Firai Ministan Garry Conille ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, “Za’a farauto wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya, ba tare da bata lokaci ba.”
Hukumomin kasar sun rufe manyan tituna da hanyoyi shiga cikin birnin da kwantenonin jigilar kaya.
Rundunar ta IDF ta fada a ranar Alhamis cewa, wani harin da Isra’ila ta kai da jiragen yakinta ya kashe wani kwamandan Hezbollah Khader Al-Shahabiya.
Domin Kari
No media source currently available