Hakan na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan Israi’la ta kashe shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, da kwamandojinsa.
Fafatawar Walz da Vance zai kasance a yau Talata 1 ga watan Oktoba da karfe 9 na dare agogon ET da Laraba 2 ga watan Oktoban da muke ciki da karfe 1 na safe agogon UTC.
A yau Talata, rundunar sojin Isra'ila ta gargadi al'ummomin dake zaune a yankunan kan iyakar Lebanon dasu kaurace daga kusan garuruwa 24 bayan da ta kaddamar da samamen da ta kira da kwarya-kwaryan kutse ta kasa akan mayakan kungiyar Hezbollah
Mummunar gobarar ta babbake motar dake kan wata babbar hanya a yankin arewacin birnin Bangkok yayin da take dauke da yara 38-da suka hada da kanana da matasa da malamai 6 dake balaguron 'yan makaranta.
Mutombo wanda aka haifa a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, da fari ya zo jami'ar Georgetown dake Washington ne a bisa tallafin karatu a shekarar 1987, sannan yayi shura sa'ilin daya shiga kungiyar wasan kwallon kwando yana shekararsa ta 2.
A yau Litinin, fadar Kremlin ta yi Allah-wadai da kisan Shugaban Hizbullahi Hassan Nasrallah da hare-haren Isra’ila ta sama su ka yi a makon da ya gabata sannan tace tana da hasashe mai karfi dake nuna yiyuwar fadadar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Hezbollah na riko ya sha alwashin ci gaba da yakar Isra’ila sannan ya bayyana cewar a shirye kungiyar take ta shafe dogon zango tana yaki duk kuwa da cewar an hallaka manyan kwamandojinta, ciki harda jagoranta, Hassan Nasrallah.
Yayin da daruruwan iyalai ke kwanciya a kan titunan Beirut, hukumomin kasar ta Lebanon sun ce mutanen da suka rasa muhallansu sun kai miliyan daya.
A yau dakarun Isra’ila suka ce sun sake kashe wani babban jami’in Hezbollah a wani hari ta sama, a daidai lokacin da kungiyar da ke Lebanon ke cikin juyayin kisan shugaban ta Sayyadi Hassan Nasrallah.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace, kalaman China da abinda ta keyi dangane da kawo karshen yakin da Rasha keyi a Ukraine sunyi halshen damo, ganin yadda gwamnatin Beijing ke cigaba da kyale kamfanonin China suna samar da mai ga injinan da Rashan ke amfani da su a yakin.
Isra’ila tace ta hallaka jagoran Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah a yayin wani hari ta sama da ta kai kan hedikwatar kungiyar dake birnin Beirut na kasar Lebanon. Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da labarin mutuwar.
Shugaba Vladimir Putin ya gargadi Amurka da kawayenta akan cewar Moscow na duba yiyuwar maida martani da makaman nukiliya matukar suka bari Ukraine ta kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka kera a kasashen yammacin duniya
Domin Kari
No media source currently available
Bilkisu Nana Hassan, wata ma’aikaciyar gwamnati da ta yi ritaya a Kaduna, ta ce mata za su iya rungumar yin noma na zamani a cikin gidajensu, ba tare da sun je ko ina ba.