Hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Amurka tace tana sane da kamen kuma babu ko guda daga cikin Trump ko mahalarta gangamin daya shiga wani hatsari a lamarin, daya afku a ranar Asabar.
Jam’iyyar ta ce daya daga cikin mambobinta ya mutu a rikicin.
Taiwan ta bada rahoton hango wani jirgin ruwan dakon jiragen yakin China da ya nufi kudancin tsibirin a ranar Lahadi.
Dakarun Isra’ila sun sanya shinge tsakanin Beit Hanoun, Jabalia da Beit Lahiya dake kuryar arewa da birnin Gaza, inda suka sanya shinge tsakanin yankuna 2, har sai mutanen da suke so su bi umarnin da aka basu su fita daga birnin da iyalan su sun nemi izini kafin su fice daga garuruwan 3.
Gwamnatin Vietnam tace, sun amince ita da China su karfafa hadin guiwa domin bunkasa sha’anin tsaro da kare kansu, duk kuwa da lokacin da suka dauka suna yar tsama da juna kan batun kogin kudancin China.
Rasha ta fada ranar asabar cewa, ta dakile hare haren jirage marasa matuka 47 da Ukraine tayi yunkurin kai mata hari da su, yayin da Kyiv itama ta bada rahoton kakkabo jirage marasa matuka 24 da Moscow ta yi yunkurin kai mata hari da su.
Hezbollah, wace ta rasa shugabanta da wasu manyan kwamandojin ta a wasu hare haren Isra’ila, tun lokacin da aka fara yaki a Lebanon, ta ce, ta kai farmaki da makaman missile wani sansanin sojin Isra’ila a kudancin birnin Haifa a ranar asabar, .
A yayin wani biki na kungiyar manema labarai masasa shinge a Landan. Dan Jimmy Lai, Sebastien yace mahaifin shi, wanda ke da takardar zama dan kasar Birtaniya, na cikin mawuyacin hali a inda yake a tsare kusan tsawon shekaru hudu.
Iyalan pasinjojin da suka gamu da ajalin su a hadduran jirgin saman Boeing 737 Max biyu, sun halarci zaman babban kotun kasa dake Texas, domin sauraren ba’asi, tsakanin lauyoyin su da masu gabatar da kara.
Iran tace, ta gano gawar wani janar din sojin juyin juya halin da aka kashe tare da jagoran Hezbollah Sayyadi Hassan Nasrallah a yayin wani harin da Izra’ila ta kai a watan jiya a Beirut.
Bikin wanda ke gudana duk ranar 11 ga watan Oktoba an fara gudanar da shi ne tun cikin shekarar 2012 kuma yana maida hankali ne wajen neman kara wayar da kan al’umma “akan yadda matsalolin sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da talauci ke shafar ‘ya’ya mata”
Isra’ila ta ce ta kai harin ne kan wata cibiyar da ake ba da umarni da ke cikin makarantar.
Domin Kari
No media source currently available