A kan hanyarsa ta dawowa daga rangadin da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya, Blinken ya gana da firaministan kasar Lebanon Najib Mikati a birnin London, wanda ya fito daga wani taro kan kasar Lebanon a birnin Paris wuni guda kafin ganawar.
Su biyun sun yi murmushi a gaban kyamarori amma ba su ce komai ba.
Amurka, dake ci gaba da kasancewa babbar kawar Isra'ila ta fannin siyasa da soji, kwatsam ta daina yin kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a cikin watan da ta yi ruwan bama-bamai kan mayakan Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran a Lebanon.
Amma dai Blinken ya yi kira ga neman hanyar diflomasiya cikin gaggawa wurin shawo kan yakin.
"Mun fito fili cewa wannan ba zai iya jagoranta ba -- bai kamata ya jagoranta ba -- zuwa ga wannan yaki da yaki-ci-yaki-cinyewa, kuma dole ne Isra'ila ta dauki matakan da suka dace don kaucewa hallaka fararen hula, kuma kada ta jefa dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ko kuma dakarun Lebanon cikin hadari," in ji Blinken jiya Alhamis a birnin Doha.
Amurka ta yi kira ga gwamnatin tsakiya ta Lebanon da ta dade tana fama da tabarbarewar tsaro da ta dauki nauyin kula da harkokin tsaro da kuma kwance makamai a hannun kungiyar Hezbollah, kungiyar Shi'a da ke samun goyon bayan Iran wacce ke da nata sojan.
Kungiyar Hezbollah ta harba makamai masu linzami kan Isra'ila tare da Hamas tun bayan harin da mayakan Falasdinawan suka kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya haifar da kazamin harin soji da Isra'ila ta kai a Gaza.
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a wata kira da ya yi ga takwaransa na Isra'ila Yoav Gallant a ranar Laraba ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da Isra'ila ta kai kan sojojin Lebanon wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Lebanon akalla 11, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya hada wasu alkaluma daga sanarwar sojojin.
Dandalin Mu Tattauna