A jiya Juma’a Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya gana da firaministan kasar Lebanon, inda suka tattauna kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a kasar, a daidai lokacin da Washington ta matsa wa gwamnatin Beirut lamba kan ta dauki mataki kan kungiyar Hezbollah.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da take yiwa Gambaryan a bisa dalilai na rashin lafiya.
Harin ya zo ne bayan sa’o’i kadan da ake zargin 'yan tawaye Kurdawa sun ta da bama-bamai da kuma bude wuta a kamfanin sararin samaniya da tsaro na TUSAS.
Netanyahu, kamar yadda rahotanni suka nuna a ganawar ta tsawon sa’o’i biyu da rabi, ya shaida wa Blinken cewa kisan Sinwar zai iya kawo “kyakkyawan tasiri” wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cimma burin Isra’ila na kawo karshen mulkin Hamas.
Blinken ya isa yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda ma’aikatar harkokin waje ta sanar cikin wata sanarwa, inda ake sa ran zai tattauna muhimmancin kawo karshen yakin da akeyi a Gaza.
Sanjay Kumar Verma, wanda aka kora a ranar Litinin da ta wuce tare da wasu jami’an diflomasiyyar India biyar, ya fada a cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na CTV a ranar Lahadi cewa zargin yana da alaka da bita da kullin siyasa.
Koriya Ta Arewa tayi ikirarin gano wasu tarkacen akalla jirgi mara matuki guda na sojojin Koriya Ta Kudu a babban birnin kasar Pyongyang, tare da kafa wasu hotunan jirgin da masu sharhi suka tabbatar cewa lallai na KTK ne.
An Kama wani dan asalin kasar Libya a Jamus, wanda ake zargi da kitsa kai farmaki ofishin jakadancin Isra’ila a birnin Berlin sannan an alakanta shi da kungiyar IS wanda za a gabatar da shi a gaban kuliya yau Lahadi, a cewar mahukunta a Jamus.
Gwamnatin Isra’ila tace, wani jirgi mara matuki ya kaikaici gidan priminista Benjamin Netanyahu a ranar Asabar. An sanar da cewa, shi da mai dakin shi basa cikin gidan a lokacin da aka kai harin.
Rundunar sojin ruwan Mexico ta bayyana yin wani wawan kamu, inda ta kwace sama da tan 8.3 na kwayoyi a ruwan pacific, kamu mafi girma a bugu daya cikin rana guda, a samamen da ta gudanar ta ruwa
Akalla mutum 21 suka mutu sanadiyyar wasu hare haren da Isra’ila ta kai, wanda suka hada da yara, bisa bayanan ma’aikatan asibiti da wani dan jarida mai aiki da Associated Press.
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ya nada wani na hannun daman shi cikin majalisar zartaswa, wanda shugaban Amurka Joe Biden yayiwa afuwa a bara, a wani musayar bursunoni, biyo bayan tabbacin cewa, Venezuela zata gudanar da ingantaccen zabe a shekarar 2024.
Domin Kari
No media source currently available