A ranar Asabar dinnan rundunar sojin ruwan Mexico ta bayyana kwace sama da tan 8.3 na kwayoyi a ruwan pacific, wani wawan kamu mafi girma a bugu daya cikin rana guda, a samamen da aka gudanar ta ruwa.
Wata sanarwa data fito daga ma’aikatar dakarun ruwa, tace, jami’an dakarun ruwan sun yi nasarar kwace kilogram 8,361 na miyagun kwayoyi, wanda ya kasance kamu mafi girma da dakarun ruwan suka taba yi a tarihi.
Ba adai sanar da takamaiman sampurin kwayoyin da aka kama ba, to amma an bayyana cewa darajar su ta kai ta kimanin dalar Amurka milyan 105.
An kama mutane 23 a yayin samamen da aka gudanar a kudu maso yamma na tashar ruwan Lazaro Cardenas dake daura da yammacin gabar ruwan Mexico.
Ma’aikatar ta kara da cewa, an rarraba kwayoyin ne cikin kananan jiragen ruwa da aka lababa su cikin wani sundukin dake tafiya ta karkashin ruwa, wanda ke da sarkarkiyar sarrafawa ga mahaya jirgin.
Kamun kwayoyi na karshe da aka yi a Mexico shine na tan 23 na hodar ibilis ta Colombia, a watan Nuwamban shekarar 2007.
Mexico ta kasance matattarar safarar miyagun kwayoyi da ake shiga dasu Amurka a gwamman shekaru, inda kungiyoyin safarar kwayoyi ke kokawar samun iko akan harkar.
Jihar Michoacan dake daura da gabar ruwan da akayi nasarar kwace kwayoyin, wuri ne da ya kasance dandamalin rikice rikice tsakanin kungiyoyin masu aikata laifuffuka, da ya hada da gagarumar kungiyar yan safarar kwayoyi ta Jalisco Nueva Generacion, wadda daya ce daga cikin kungiyar masu aikata laifuffuka mafi karfi a Mexico.
Samamen na baya bayan nan da aka ruwaito a ranar Juma’a, an gudanar da shine kwanaki biyu da suka wuce, da jami’ai suka gudanar ta kasa, da wasu da suka mara musu baya ta sama, cewar ma’aikatar.
Haka zalika an samu litar man fetur 8700 cikin sundukan jirgin a yayin samamen , wadda itama wata harka ce da kungiyoyin safarar kwayoyin ke tabawa.
A ranar 23 ga watan Agusta, hukumomi sun ruwaito cewa, sun kama kimanin tan 7 na miyagun kwayoyi a wasu samame biyu dabam dabam, da aka gudanar a wuri guda da aka yi na wannan karon a kasar.
Rundunar ruwan Mexico wadda kan gudanar da aikin sa ido akai akai, ta rika gano hanyoyi dabam dabam da ake safarar kwayoyi ta ruwa, da ya hada da wani na hodar ibilis da aka zuzzuba cikin garewanin nikakken barkono guda 217 a shekarar 2016.
Dandalin Mu Tattauna